Babban Fasto na cocin RCCG, Pastor Enoch Adebayo ya yi martani kan wani hotonsa da ke yawo a kafafen sada zumunta dake nunashi a kasar Saudiyya yaje aikin Hajji.
Yayi martanin ne ranar Asabar, 4 ga watan Janairu a yayin bikin shiga sabuwar shekara.
Yace nasan kunga hotona da aka nunani kamar Alhaji,… daga nan aka fashe da shewa a cocin nasa, saidai bai sake cewa komai ba, ya ci gaba da sha’aninsa.
Da ganin wannan hoto dai na bogene.