Friday, December 5
Shadow

Babban Malamin Kirista, Reverend Ezekiel Dachomo na san Suka har daga wajan Kiristoci saboda kiran Addinin Musulunci addinin Qarya

Malamin Kirista, Reverend Ezekiel Dachomo ya mayarwa da Sheikh Dr. Ahmad Gumi da martanin cewa da gaske an binne Kiristoci da yawa wanda ake zargin ‘yan Bindiga da kashewa.

Hakan na zuwane bayan da Rahotanni suka bayyana cewa, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya zargi Kiristoci da binne akwatunan gawa a karya da babu gawar a ciki dan su nuna cewa, an kashe musu mutane.

Faston ya kai ziyara wani kabari da aka binne mutane 27 kamar yanda yace inda anan ne yace zasu sa matasa su hako gawarwakin dan a nuna shaida.

A cikin jawabinsa ne yake cewa Addinin Musulunci addinin Qarya, Subhanallah.

Saidai wasu hadda Kiristoci sun bayyana cewa abinda ya fada bai kamata ba, bai kamata bacin ran abinda Sheikh Gumi ya masa ba yasa ya bayyana gaba dayan Addinin Musulunci da addinin Qarya ba.

Karanta Wannan  Idan ADC ta tsayar dani takara babu shakka zan kayar da Shugaba Tinubu zabe a 2027>>Rotimi Amaechi
https://twitter.com/ChuksEricE/status/1989442363454816751?t=qzqu2-syFbVTDaycvCpbKw&s=19

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *