Monday, December 16
Shadow

Babu Mutumin Da Yake Da Ikon Hargitsa Mana Kasa Saboda Gwamnati Ta Cire Tallafin Man Fetur, Cewar Dr Jalo Jalingo

Babu mutumin da yake da ikon hargitsa mana Kasa a Shari’ance saboda Gwamnati ta cire tallafin man petur, ko saboda hauhawar farashin kayayyaki, ko saboda tsadar rayuwa, ko saboda ba dan Arewa ba ne yake yin mulki, ko saboda ba wanda yake so ba ne yake yin mulki, ko saboda hauhawar jahìĺçìnsa a fùskar addini.

Masu rinjaye cikin ‘yan Nijeriya suna da ikon kawar da mulkin APC a zaben 2027, kamar yadda suka taba kawar da mulkin PDP a 2015, wannan kuma ba wani abu ba ne sabo a irin wannan tsarin mulki da wannan Kasa tamu take kansa.

Muna kara nanata cewa sam ba daidai na a samu wasu sakarkaru cikin samari su karya doka da oda su wulakanta ramzin Kasa, ko su lalata dukiyar Gwamnati, ko su lalata dukiyar daidaiku, sannan kuma hukuma ta kama su domin hukunta su, sai kuma a samu wasu da za su rika cewa abin da suka yi din daidai ne, ko kuwa matakin Gwamnati ta dauka a kansu ba daidai ba ne!!Tabbas wannan al’amari abin takaici ga mahankalta.

Karanta Wannan  Mun baku wata daya ku sauko da farashin kayan abinci ko mu daureku>>Gwamnatin Tarayya ga 'yan kasuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *