Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa, bata tunanin hadewa dan yin maja da kowace jam’iyya.
Hakan na zuwane yayin da ake tsammanin Atiku da Peter Obi zasu hade dan hada karfi su kayar da jam’iyyar APC.
Hakanan a bangaren Labour party, shima kakakin kungiyar yakin neman zaben Peter Obi, Yunusa Tanko ya bayyana cewa Peter Obi baya tunanin hadewa da kowa dan samun karfi.
Jam’iyyar PDP tace bata neman hadewa da kowa amma tana maraba da tsaffin membobinta wanda suke son dawowa cikinta.
Kakakin PDP, Debo Ologbunagba ne ya bayyana hakan inda yace a rijistar da suke yi yanzu haka, mutane da yawa a matakin mazabu sai shiga PDP suke wanda hakan alamace ta cewa har yanzu PDP jam’iyyar Al’ummace.