
A jiya ne dai hutudole ya kawo muku Rahoton cewa, wani masoyin marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya maka Baffa Hotoro a kotu saboda kalaman da yayi kan malamin.
Mutumin dai a baya ya baiwa Baffa Hotoro kwanaki ya janye kalamansa akan malam sannan ya bayar da hakuri ko kuma ya kaishi kotu.
Saidai Baffa Hotoro bai janye kalaman nasa ba sannan bai bayar da hakurin ba, dalilin hakane yasa mutumin ya maka Baffa Hotoro a kotu.
Saidai kwana daya bayan faruwar hakan, an ga wani Bidiyo na Baffa Hotoro yana cewa shi bai ce Dahiru Bauchi dan Wuta bane sannan bai kirashi da Kafuri ba.
Yace kawai dai ya bayyanashi a matsayin jahili wanda ya karantar da a bi Inyasi maimakon Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam).