Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana farin cikinsa da sakin kananan yara da aka kama bisa zargin cin amanar kasa.
Gwamnan yace bai san an kama yaran ba sai bayan da aka kaisu gaban kotu a Abuja.
Ya bayyana hakane a Asibitin Muhammadu Buhari Special Hospital inda aka kai yaran dan a dubasu a tabbatar suna cikin koshin lafiya.
Gwamnan ya kuma godewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kan yafewa yaran inda yace zai tabbatar an sada su da iyalansu sannan a tabbatar sun koma makaranta dan Inganta rayuwarsu.