
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa, shuwagabannin Najeriya da suka zo bayan Obasanjo ne ke da Alhakin dawowar Kungiyar Bòkò Hàràm.
Ya bayyana hakane a Abuja a yayin ziyarar da wasu ‘yan siyasa daga jihar Kogi suka kai masa.
Yace kungiyar ta fara bayyanane a shekarar 2002 a jihar Yobe
Yace suna sumun labari, Obasanjo ya aika aka kirashi yace mai ya yake ganin za’a bullowa wannan lamari? Sai yace masa a kira shuwagabannin tsaro a basu lokaci su gama da kungiyar, idan suka kasa sai a sauke su a nada wasu.
Yace haka kuwa aka yi kuma aka murkushe kungiyar.
Yace bayan sun sauka Mulki ne wanda suka hau suka yi sakaci kungiyar ta dawo.