
Wanda ke ikirarin cewa shine shugaban jam’iyyar ADC, Nafiu Bala wanda kuma ya kai su Atiku, Kwankwaso, Peter Obi, da David Mark, da Rauf Aregbesola da sauransu kotu yana neman a kwace shugabancin jam’iyyar a bashi watau Nafiu Bala yace bai taba ganin zalunci irin na su Atikun ba.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi wadda ta watsu a kafafen sada zumunta.
Yace ta yaya mutane zasu zo har gidansa su sameshi suce zasu yi fada dashi kuma su yi nasara?