
Sabon Ministan tsaro, Janar Christopher Musa ya bayyana cewa, bai yadda da yin Sulhu da ‘yan Bindiga ba.
Yace suna amfani da yin sulhu ne kawai su samu kara sayen makamai da kuma samun kudi.
Yace yawanci garuruwan da aka yi sulhu da ‘yan Bindiga sukan koma su ci gaba da kaiwa mutane hari daga baya.