
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, baya nuna bangaranci a gwamnatinsa inda yace ya fi baiwa ‘yan Arewa mukami fiye da ‘yan kudu.
Shugaban ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa Sunday Dare.
Yace Shugaba Tinubu ya baiwa ‘yan Arewa 71 mukami a ma’aikatun gwamnatin tarayya daban-daban sannan ya baiwa ‘yan kudu su 63 mukamai.
Yace ko lokacin yana gwamnan Legas, Shugana Tinubu ya haiwa wanda ba ‘yan legas ba mukami a gwamnatinsa.
Sannan yace har yanzu gwamnati bata kare ba, za’a ci gaba da bayar da mukamai nan gaba.