
Matar tsohon gwamnan Kaduna, Hajiya Hadiza Ismail El-Rufai ta musanta wani rahoto dake cewa ta rigamu gidan gaskiya.
Tace ba ita bace, ita ba zata mvtv ba inda tace ita Allah zai barta.
Ta rubuta hakane a shafinta na X.
Hon. Bello El-Rufai dai ya wallafa cewa matar dan uwan mahaifinsu ta rasu.
Inda daga nan ne masu rahoton suka samu matashiyar labarin suka wallafa ba tare da bincike ba.