Wednesday, January 15
Shadow

Basir ga mai ciki

Basir ga mata masu ciki ba sabon abu bane, wani bincike ya gano cewa,duk cikin mata masu ciki 3 ana samun macen dake da basur 1.

Mata masu ciki na fama da basir saboda yanda jikinsu ke budewa dalilin daukar ciki da nauyin dan suke dauke dashi.

Yawanci basir din mata masu ciki yana farawa ne a yayin da cikin ya fara nauyi,watau daga wata na 3 zuwa sama.

Masana kiwon lafiya sun bayar da shawarar cewa,idan a baya kin taba cin basir yayin da kike da ciki,yana da kyau ki nemi shawarar likita a yayin da kika kara samun ciki.

Maganin basir ga mai juna biyu

Ga hanyoyin magance basir ga mai juna biyu kamar haka:

Karanta Wannan  Alamomin cikin wata tara

A canja tsarin cin abinci: Canja tsarin cin abinci ta yanda za’a rika cin abinci me dauke da fiber,watau dusa, da kuma abinci me ruwa-ruwa, da shan ruwa akai-akai zasu taimaka wajan maganin basir ga mai juna biyu.

Ana iya cin masara wadda ba’a sirfa ba, ko a yi kunun gero, dawa, alkama, wadda ba’a airfaba, cin aya, kwakwa da sauransu zasu taimaka sosai.

Idan basir me tsiro ne, a dora kankara akan tsiron ko kuma a zauna a cikin ruwa me dumi, hakan zai taimaka matuka.

Shan magungunan rage radadi kamar Paracetamol zai taimakawa mace mai juna biyu dake fama da cutar basir.

Amfani da man shafawa wanda ake shafawa da turawa a cikin dubura na basir shima yana taimakawa matuka wajan magance ciwon basir ga mata masu juna biyu.

Karanta Wannan  Cikin wata hudu

Basir din mace mai ciki zai iya taba dan cikinta?

A ilimin likita, basir din mace mai ciki ba zai taba dan dake cikinta ba.

Saidai a yayin da kika zo haihuwa, basir din zai iya munana, dan haka yana da kyau a tuntubi likita ko ungozoma.

Hakanan masana sunce bayan haihuwa, basir din dake damun mace mai ciki ya kamata ya warke.

Idan bai warke ba, a tuntubi likita.

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *