
A karon farko, hukumomi a Najeriya suka fito a bainar jama’a suka yi watsi da wata buƙata da suke zargin Amurka ta bijiro musu, ta neman amincewar Najeriya ta karɓi wasu ƴancirani na ƙasar Venezuela da Donald Trump ke son tasa ƙeyarsu daga Amurkar bayan fito da su daga gidan yari.
Hakan ne ya sa ƴan Najeriya da dama ke tambayar haƙiƙanin abin da ke faruwa tsakanin ƙasashen biyu.
Wannan na zuwa ne ƴan kwanaki bayan da Amurka ta taƙaita bai wa ƴan Najeriyar biza baya ga ƙarin haraji kan kayayyakin da Najeriya da wasu ƙasashe ke shigarwa zuwa Amurkar.
Sai dai wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka a Naejriya ya fitar ta ce “matakin da Amurka ta ɗauka game da bayar da biza bai da alaƙa da matsayar kowace ƙasa kan baƙi” da Amurka ke kora “ko kuma alaƙa da wasu ƙungiyoyi kamar BRICS”.
Wani batun da ya ƙara wa ƴan Najeriya tunanin ko akwai wani abu tsakanin Amurkar da ƙasar tasu, shi ne yadda a farkon makon nan shugaban Amurka Donald Trump ya gayyaci wasu ƙasashen Afirka guda biyar zuwa fadar White House ba tare da Najeriya ba duk kuwa da cewa ita ce ƙasa mafi yawan al’umma, kuma ɗaya daga cikin mafiya ƙarfin tattalin arziƙi a nahiyar.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar ya shaida wa BBC cewa ba za su amince da buƙatar Amurka ta ƙara wa ƙasar matsalar tsaro ba.
“Wannan al’amari dai yana da matuƙar mamaki da al’ajabi a gare mu cewa ana so lallai sai mu karɓi ƴan ƙasar Venezuela fursunoni waɗanda za a fitar da su daga Amurka saboda laifuka da suka yi kuma an riga an kasafta cewa ana so Najeriya ta karɓi wasu daga cikinsu.”
“Mu kuma mun ga cewa lallai ba zai yiwu ba a dokar Najeriya. Mun duba mun gani cewa mutanen nan farare ne sannan ba harshenmu suke ji ba kuma yaya za a yi mu bari a ɗebo masu laifi daga wata ƙasa a kawo mana duk da irin matsalar tsaron da mu ma muke fama. Sun ce mutum 300 ne za a kawo mana.”
“Mu ba mu yarda ba duk kuwa da barazanar cewa za a ƙara mana haraji kan kayan da muke shigarwa Amurka sannan kuma za a daina ba mu biza idan ba mu yarda ba.”
Dangane da batun bayar da biza, a ranar 8 ga watan Yulin nan ne Amurka ta sanar da wasu jerin tsauraran sauye-sauye a tsarin bayar da takardar izinin shiga ƙasarta ga masu zuwan wucin-gadi daga Najeriya.
A yanzu ƙasar ta zaftare wa’adin bizar da kuma dalilan bayar da bizar ga yawancin ƴan Najeriya.
Amurka ta ce ta ɗauki matakin ne domin yin ramako ga daina bayar da bizar da Najeriya ta yi wa wasu Amurkawa na tsawon lokaci, iƙrarin da hukumomi a Najeriya suka musanta.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurkar ta ce manufofi da tsare-tsaren bayar da biza na daga abubuwan da ake iya sauyawa a kodayaushe – wanda kuma za a iya sauya shi la’akari da yanayin alaƙar diflomasiya da tsaro da ƙa’idoji ko yanayin shige da fice.
A sanarwar gwamnatin Amurka ta ce tana aiki ƙut-da-ƙut da hukumomin Najeriya domin tabbatar da ganin Najeriya ta daidaita al’amuranta kamar yadda ya dace da tsarin manyan ƙasashen duniya – ta fannin
Ƴan Najeriya masu yawon buɗe idanu da ƴan kasuwa masu tafiye tafiye na daga cikin waɗanda wannan sauyi mai tsauri na bayar da bizar Amurkar zai shafa.
Cikin sanarwar ɗaukar matakin da amurka a fitar ta ce ta yi hakan ne saboda ita ma Najeriya, abin da take yi wa Amurkawa kenan.
Ƙarin haraji kan Najeriya
Najeriya na cikin jerin ƙasashen duniya da suka fuskanci sabon ƙarin haraji da Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya wa kayayyakin da ƙasashen duniya fiye da 50 ke shigarwa Amurka.
A farkon watan Afrilu ne Trump ya sanar da sanya wa Najeriya harajin kashi 14 cikin 100 na kayayyakin da take shigarwa Amurka.
Matakin na zuwa ne a lokacin da tattalin arzikin duniya ke cikin wani hali, wani abu da masana ke fargabar cewa zai ƙara haddasa tashin farashin kayyaki a duniya.
Da fari Shugaba Trump ya sanya harajin kashi 10 kan duka kayayyakin da ake shigarwa Amurka, da kuma ƙarin harajin “ramuwa” kan gomman ƙasashen Afirka da suka sanya haraji kan kayayyakin Amurka.
Me hakan yake nufi?
Ambasada Sulaiman Ɗahiru, tsohon jakadan Najeriya a Sudan ta Kudu ya ce wannan ba wata matsala ce da za a ce ƙasashen biyu na zaman tankiya ba domin Najeriya ba sa’ar Amurka ba ce sannan kuma ita Najeriya ta fi buƙatar Amurka fiye da yadda Amurkar ke buƙatar Najeriya.
“Mu muke buƙatar Amurka ba Amurka ce ke buƙatar mu ba. Dole a tattauna dangane da yadda za a sasanta matsalar. Ministan harkokin wajen Najeriya ya kamata ya tashi ya je Amurka ya je ya ga sakataren harkokin wajen Amurka domin a sasanta.” In ji amabsada Sulaiman Dahiru.
Ya ƙara da cewa akwai lokutan da ake samun irin wannan saɓani kuma tattaunawar diflomasiyya ce kawai za ta samar da fahimtar juna.
Sai dai kuma ya ce akwai wasu matakan da ɗaukar su na nuni da alamun raini daga ƙasashen duniya ciki kuwa har da ƙasashen Afirka.
“Idan an ɗauki Najeriya da ƙima yadda ya kamata to ba za a yi wa ƙasar haka ba. Lokacin da Najeriya take Najeriya babu wata ƙasa da za ta iya yi wa Najeriya shakiyanci ba. Amma yanzu da al’amura sun lalace a Najeriya ko ƙasashen Afirka ma kallon raini suke yi mana ballantana Amurka.” In ji ambasada Sulaiman.