Tuesday, March 17
Shadow

Bazan goyi bayan Gwamnatin Tinubu ba>>Sarki Sanusi II

Me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa ba zai taimakawa Gwamnatin Tinubu da shawarwarin gyaran tartalin arzikin Najeriya ba.

Ya bayyana hakane a wajan taron tunawa da babban lauya, Gani Fawenhinmi a jihar Legas.

Yace gwamnatin ta kasa samun wanda zai fito yawa mutanen Najeriya jawabi akan alfanu da dalilin tsaretsaren da ta kawo dake jefa mutane a matsalar matsin rayuwa.

Sarki Sanusi yace mutanen dake cikin gwamnatin abokansa ne amma kuma basu nuna girmama abotar tasu ba dan haka ba zai taimakawa gwamnatin ta hanyar tayar da komadar tattalin arzikin kasarnan ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon:Yanda tsohon shugaban kasar Fransa Nicolas Sarkozy ya fara zaman gidan yari na shekaru 5 bayan da aka sameshi da laifin karbar kudin yakin neman zabe ta hanyar da bata dace ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *