Friday, December 5
Shadow

Bidiyo Da Duminsa: Kalli yanda aka rantsar da Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC

Jam’iyyar APC ta naɗa Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa, bayan taron da aka gudanar a Abuja tare da shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jam’iyyar.

Yilwatda, wanda ya fito daga jihar Filato, ya maye gurbin Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda ya yi murabus a watan Yuni 2025 saboda dalilan lafiya. Kafin naɗinsa, Yilwatda na rike da mukamin Ministan Jin ƙai da Rage Talauci a gwamnatin Tinubu.

Farfesa Nentawe ya kasance ɗan takarar gwamna a jihar Filato a zaɓen 2023 karkashin APC. Hakanan, ya taba zama kwamishinan zaɓe na hukumar INEC daga 2017 zuwa 2021, inda ya jagoranci harkokin zaɓe a jihohi da dama.

Karanta Wannan  Kalli hotunan mata 'yan kwallon kasar Zimbabwe da mutane ke cewa suna kama da maza

Naɗin nasa ya zo ne da nufin ƙarfafa haɗin kai da daidaiton wakilci a jam’iyyar, kasancewar yankin Arewa ta Tsakiya ke da hakkinta a kujerar shugaban jam’iyya. Hakanan kasancewarsa Kirista na ba da gudunmawa wajen daidaita wakilcin addinai a cikin jam’iyyar.

Jam’iyyar APC na fatan sabon shugaban zai sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, tare da kawo zaman lafiya da tsari a jam’iyyar, musamman yayin da ake shirin fuskantar zaɓen 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *