Wata sabuwar cuta ta sake bulla a kasar China me suna HMPV Virus.
Cutar kamar dai Corona Virus itama na da alaka da sarkewar numfashi amma tafi kama kananan yara ‘yan kimanin shekaru 14.
A kasar Chinan, an dawo da irin dokar da aka yi lokacin da cutar CoronaVirus tazo, watau saka Face Mask da yin nesa-nesa da juna da sauransu.
Saidai wani abin jin dadi shine wannan sabuwar cutar bata kai Coronavirus illa ba.
A ranar Lahadi, Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar fara daukar matakin killacewa da kuma binciken lafiya ga dukkan mutanen da suka shigo Najeriya daga kasar China.
Wannan cuta dai na zuwane shekaru 5 bayan bullar cutar Coronavirus.
A kasar China, Asibitoci aun cika da mutanen da suka kamu da wannan sabuwar cuta inda ake ta yada hotuna da bidiyo a kafafen sada zumuna.
Comment zancen banza da wofi,shugabanni suna kirkirar cututtukane dan neman duniya.ai ko corona ma karyace