Yahudawan Israela sun yi wani abin ban mamaki da ya dauki hankulan Duniya.
A ci gaba da yakin da suke da Falasdinawa, sanannen abune cewa, Hezbollah sun shigarwa Falasdinawan fadan inda suka ce idan ba’a daina kashe Falasdinawan ba suma ba zasu daina fada da Israela ba.
A hakanne kasar Israela ta tayarwa da mayakan Hezbollah da bamabamai a cikin wayoyinsu.
Akalla mutane Dubu 2 ne suka jikkata sadaniyyar tashin wadannan bamabamai a fadin kasar ta Lebanon ciki hadda wakilin kasar Iran a Lebanon din kamar yamda wasu rahotanni suka bayyanar.
Saidai duk da lamarin tayar da bamabamai din ya dauki hankula, abu daya da aka rika tambaya shine,wai me yasa kasar Israela ta rikawa falasdinawa kisan kiyashi idan dai zata iya amfani da irin wannan hanyar dan kashe wadanda take so?
Watakila amsar wannan tambayar itace Hezbollah tafi Hamas karfi wadda idan Israela tace zata yi fada da ita na kai tsaye, itama zata ji a jikinta.