Thursday, October 3
Shadow

Ko Kun Kula Cewa Hussaina Matar Soja Abbas Bai Karbu Sosai A Wajen Matan Sòšhìýal Mìďìýa Ba, Duk Da Cewa Labarinta Yana Da Sosa Zuciya?

Ko Kun Kula Cewa Hussaina Matar Soja Abbas Bai Karbu Sosai A Wajen Matan Sòšhìýal Mìďìýa Ba, Duk Da Cewa Labarinta Yana Da Sosa Zuciya?

Daga Abba Audu Abba

Dalilin da ya sa labarin bai yi trending ba a wajensu shine kawai :

  1. Ita Hussaina mutumiyar kirki ce. Su kuma galibi ba haka suke ba. Yawancin su sun fi karkata ga abinda yake na šhìŕìrita ko kuma yake dauke da sharri musamman akan zamantakewar aure.
  2. Ita Hussaina mace ta gari ce wacce ta san mutunci da darajar miji sannan ta san darajar aure. Su kuma ģaĺibi ba haka suke ba. Ba sa ganin aure a bakin komai indai akan son zuciyarsu ne.
  3. Ita Hussaina ta yadda akan mijinta ta fuskanci ko wani irin wulakanci. Su kuma galibi ba su yarda da hakan ba, saboda ba sa ganin miji a bakin komai.
  4. Ita Hussaina ta yadda ta sadaukar da kome indai akan mijinta ne. Su kuma ba su yadda da haka ba. Abinda suka yadda da shi shine, saidai miji a ko yaushe ya kasance mai sadaukarwa gare su ba dai su ba.
  5. Labarin Hussaina ba labari bane dake nuna rashin mutunci da rashin kirkin maza ga matansu. Su kuma Idan labari ba ya bayyana maza a matsayin ažžàĺùmaii marasa kirki, ba sa so kuma ba sa kai hankalinsu wajen.
Karanta Wannan  Ginin Masallaci Ya Rufťò Kañ Masallata A Jìhar Lagos, Inda Ake Kyautata Zaton Jama'a Sun Ŕàśà Ŕàñśù

Wadannan sune dalilai da suka sa labarin Hussaina ba ya trending a wajen galibin mata a social media, musamman wadanda suke daukar kanau masu ‘ýañçi.

Da a ce Hussaina labari ta bayar akan, misali, cewa mijinta àźźĺumi ne. Yana dukanta. Baya ciyar da ita balle tufatarwa. Ko kuma ya ķàšhe mata ‘ya’ya da dai abu makamancin haka, Tabb! Za ka yi mamakin yadda abin zai yi mugun trending a hannun matan social media, especially yan feminism. Za su kakkara abinda zasu kara sannan suyi ta yadawa a kafa-kafa. Ba dan komai ba, saboda su bayyanawa duniya cewa ai duk maza haka suke mutane ne marasa kirki.

Karanta Wannan  Taron Barayine a cikin gwamnatin Najeriya ta yanzu dan haka kada kuyi tsammanin su kawo muku gyara>>Inji Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo

Za ku yadda da ni akan wannan idan kuka tuna yadda matan social media suka yi ta yuyuyu da yayata labarin karya da aka bayar kwanannan wai wani miji ya saki matarsa tana tsakiyar naķuda a asibitin Aminu Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *