Tauraron dan Tiktok kuma mawaki, G-Fresh Al’amin yayi rokon Allah ya bashi diya kamar Murja Kunya.
An ganshi a wani Bidiyo ya daga hannuwa sama yana rokon Allah ya bashi diya irin Murja.
G-Fresh ya kuma yi fatan cewa duk abinda yake yi, yana son dansa shima yayi.
Kalli Bidiyon anan:
G-Fresh dai na daya daga cikin mutanen da suka fi daukar hankula a shafin na Tiktok shi da murja Kunya.
Da yawa dai na Allah wadai da abinda Murja Kunya ke yi a shafin na Tiktok inda kwanannan sai da aka kamata har aka kaita Asibitin Mahaukata a Kano.
Saidai daga baya ta bar Kano inda tace ita da garin har Abada.