
An ga Bidiyon shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na karkarwa a yayin da yake sakkowa daga dandamali bayan kaddamar da yakin neman zabensa a Kaduna.
Bidiyon ya karade kafafen sada zumunta inda akai ta cece-kuce.
Daya daga cikin wadanda suka yi magana akan Bidiyon, akwai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore.
Yace dama ya fada a baya cewa shugaban kasar bashi da lafiya ya samu cutar shanyewar rabin jiki amma ba’a gaskatashi ba.
Yace amma gashinan gaskiya ta bayyana a Kaduna.