Tuesday, July 21
Shadow

Bidiyon: Wata mata ta kai Malamin Addinin Islama dake Kaduna, Sheikh Tukur Almanar Berekete Family kan zargin ya musu kwacen Fili ita da ‘ya’yanta

Wata mata ta kai babban malamin addinin Islama dake Kaduna, Sheikh Tukur Almanar gaban gidan talabijin din Brekete Family inda take zargin shi da matarsa sun mata kwacen Fili.

Tace Mijinta ne ya sayi Filin ya barwa ‘ya’yansa mata Gado inda ita kuma matar Almanar daga baya aka kaita aka sayar mata da filin.

Tace amma an je wajan Sarki da ya sayarwa da matar Almanar fili yace shi ba filin marayunnan ne ya sayar mata ba, wanine amma ita ta dage tace wannan Filin marayun take so.

Tace daga baya Almanar yace matar ta sayar masa da filin.

An kira malam inda yace ba zai ke Brekete Family ba saidai lauyansa ya je.

Karanta Wannan  DJ ya dakatar da kida bayan da aka hanashi Abinci a wajan taro

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *