
Wani nankusa da shugaban kasa Bola Tinubu kuma wanda shine mawallafin jaridar The Nation, Sam Omatseye ya bayyana cewa, Shugaba Buhari ya munafurci Bola Ahmad Tinubu.
Yace bai fito ya gayawa Tinubu cewa, ba zai yishi ba, amma kuma haka ya ce babu wanda yake goyon baya amma ya goyi bayan sanata Ahmad Lawal a boye.
Yace ba abinda Buhari yayi sai tara makafin magoya baya wanda ke shan ruwan kazanta dan nuna soyayya a gareshi.
Yace Buhari bai gyara barnar da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi ba sai ma kara lalata kasar yayi ya jefata a tsananin Bashin Naira Tiriliyan 30.
Yace Buhari kamin ya sauka daga Mulki kara lalata Najeriya yayi ba gyarata yayi ba.