Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya koma kasar bayan gurfana a gaban wata kotu a birnin Paris na kasar Faransa.
Cikin wani bidiyo da tsohon mataimakinsa na musamman kan harkokin sadarwa, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya nuna lokacin da tsohon shugaban kasar ke sauka daga jirgi a jihar Katsina.
A farkon makon nan ne tsoffin shugabannin Najeriya biyu, Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari suka bayyana a gaban wata kotun cinikayya ta ƙasa da ƙasa da ke birnin Paris na a ƙasar Faransa domin ba da bahasi dangane da kwangilar aikin gina cibiyar samar da wutar lantarki ta Mambilla da ke jihar Taraba.
Wani kamfani mai suna Sunrise Power ne dai ya kai gwamnatin Najeriya ƙara kan saɓa ƙa’idojin kwangilar, inda yake neman gwamnatin ta biya shi dalar Amurka biliyan biyu da miliyan 300 a matsayin diyya na asarar da aka janyo masa.
Tsoffin shugabannin biyu, sun bayar da shaida kan abin da suka sani dangane da kwangila da aka bayar da ita a 2003, lokacin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo.