DARASI: Shekararsa 116 Amma Babu Gigin Tsufa A Tattare Da Shi Saboda Kullum Yana Cikin Lazimi Da Ibada
Idan ka kiyaye Allah a lokacin ƙuruciya sai Ya kiyayeka a lokacin tsufa!
Na samu ganawa da Baba Malam mai shekaru dari da sha shida (116) mazaunin unguwar Tudun Murtala dake karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano.
Ba gigi ko firgicin tsufa a tare da shi, kullum yana cikin lazumi da Ibadar Allah.
Allah ya ƙarawa Malam lafiya ya ja ƙwana da albarka.
Daga Mustapha Dan Magyazo