Saturday, December 14
Shadow

Abinci

Yadda ake miyar dage dage

Abinci
MIYAR DAGE DAGE Tattasai Tumatir Albasa Attaruhu Man gyada Maggi Curry Gishiri Nama Kaza ko naman saniya /rago ko tunkiya Thyme Yadda za'a Hada a farko za ki tafasa namanki da gishiri, albasa, maggi, thyme. Ki wanke kayan miyarki a markada, attaruhun ki sa ka kadan don ya kara dandanon miyar. Bayan kin tafasa naman sai Ki soya shi ki kwashe naman sai ki zuba kayan miyar ki soya ki kwashe naman ne don kar ya nuna sosai. Ki zuba dukkanin ingredient dinki yadda ki ke so, sai ki mayar da soyyayen naman a ciki ki hade da ruwan tafasahen naman ki yanka albasa wadatacce ki zuba, sai ki bar shi ya turara minti uku zuwa biyar. Kamshi zai yi ta tashi sai ki sauke a cikin da farar shinkafa.

Yadda ake fanke mai dadi

Abinci
YADDA AKE FANKE Bota Kwai Madarar fulawa Fulawa Sukari Bakar hoda/ Yeast Gishiri kadan Filebo HADAWA:A samu fulawa a tankade ta sannan a jika sukari a dama da ruwa kadan a kofi a yi ta gaurayawa har sai ya narke. A zuba fulawa a kwano, a zuba bota kamar cokali 2, a dirza ta da fulawa har sai ta bata a cikin fulawa. Sannan a zuba yeast kamar cokalin shan shayi biyu a ruwan dumi a jira na kamar minti 5, bayan minti 5 za a ga ya dan yi kumfa a saman kofin. Sannan a zuba madarar fulawa da gishiri rubu’in cokalin shan shayi da filebo, a fasa kwai kamar biyu. Sannan a ci gaba da murzawa. A zuba ruwan yeast a kwaba sannan, a dauko ruwan sukarin nan a zuba ana kwabawa har sai yadan yi kauri haka daidai kwabin fanke. Bayan sun kwabu sosai. Sai a rufe na tsawon yini g...

Shinkafa da wake da mai da yaji

Abinci
Shinkafa Cupi biyu cup Wake rabin Dan gishiri Albasa Man gyada Tumatir Yaji dakan hannu Maggi Salak Cucumber Dan lemun tsami Da farko na dafa waken almost ya kusan nuna. Idan ba pressure pot idan zan dafa wake Ina yayyanka albasa akai kam na dafa yana da shi ya nuna da sauri Na wanke shinkafata na zuba akai tare da gishiri. Sai ki rufe. Har sai ya dahu Zaki yayyanka Albasarki iya yadda kikeso sai ki soya da mai Sai ki yayyanka lettuce dinki dasu cucumber da tumatir. Daman already kin Riga da kin wanke su Shikenan sai a sauke shinkafar a zuba a plate tareda sosayyiyar albasa da mai sai a zuba salak din aci dadi lfy a kira da lemu mai sanyi ko ruwan sanyi

Yadda ake gurasar fulawa

Abinci
KALOLIN YADDA AKE GURASA GURASAR TANDERU KAYAN DA ZA KI TANADA Fulawa Yis Kantu/ridi Sikari gishiriYADDA ZA KI YIKi sami fulawarki ki tankade ki zuba mata yis, ki zuba ruwa ki kwaba, ka da ki kwaba shi da ruwa, ki kwaba shi da dan tauri. Idan kina son Gurasa mai sikari, sai ki zuba sikari a cikin kwabin , idan kuma kina son mai gishiri ne, sai ki zuba gishiri a cikin kwabin. Idan lokacin zafi ne za ta yi saurin tashi saboda dama yis zafi yake so ,awa uku zuwa hudu ya ishe shi ya tashi , amma idan lokacin sanyi ne yakan dade bai tashi ba. Idan kina so ki yi Gurasa da safe, to sai kin kwaba fulawarki tun da daddare, kuma kin nemi wuri mai dumi kin saka kin rufe sosai domin ya tashi. Idan kin tabbatar kwabinki ya tashi , sai ki zuba karare a cikin Tanderu, ki kunna wuta ...

Yadda ake miyar alayyahu

Abinci
YADDA AKE MIYAR ALAYYAHU. Abubuwan da ake bukata:AlaiyahoDafaffafiyar gandaDafaffafen kayan cikiDafaffafen kwai (ki bare bawon)Dafaffafen kifiGanyen koriAlbasaDafaffen markadadden kayan miyaTumatir na gwangwaniKayan kamshiSinadarin dandanoMan gyadaLawashi HADAWA:Ki gyara Alayyahu, amma ba sai kin yanka ba, sai ki wanke da gishiri ki zuba mishi tafasashshe ruwan zafi ki rufe nadan wani lokaci; Sai ki tace a ajiye a gefe. Dora tukunya a wuta ki sa man gyada ki yanka albasa ki soya sama-sama, sai ki kawo tumatir na gwangwani ki sa ki juya ki soya sama-sama. Sai ki dauko dafaffafen kayan miya ki zuba a ciki ki juya ki rufe zuwa wani lokaci. ADAMSY'S KITCHEN AND MEDICINEWHATSAPP:08051115383, 08036066553,08093651535.. Dauko ganda, kayan ciki, kifi, kayan kamshi, sinadarin danda...

Yadda ake miyar kuka

Abinci
YADDA AKE MIYAR KUKA KukaAttaruhuDaddawaAlbasaBandar kifiNamaMagiMan ja Da farko za a ɗora ruwa a wanke nama, sai a yayyanka masa albasa da gishiri kadan. Sannan a rufe ya yi ta dahuwa har sai naman ya yi laushi sai a sauke a ajiye a gefe. A ƙara ruwa kaɗan a kan silalen romon naman, sannan a yayyanka albasa sai a daka daddawa a zuba da jajjagen attaruhu mai tafarnuwa. A wanke bandar kifi a zuba. Su yi ta tafasa har sai bandar ta dahu, sannan a zuba magi da manja a rufe su ƙara tafasa. Bayan haka, sai a zuba kuka kaɗan, a riƙa kaɗawa ko da maburgi ko cokali domin kada a samu gudaji a ciki. Sai a ɗan rufe bayan ya ɗan tafasa sai a sauke.

Yadda ake wainar shinkafa

Abinci
KOYON WAINA A SAUKAKE Farar shinkafa Fulawa Baking powder Yeast Mangyada Gishiri da sugar Albasa Dafarko zaki jika shinkafarki, saiki wanke kiyanka albasa aciki kibayar a markado Saiki saka yeast, flour, baking powder, gishiri da sugar kirufe saikisa a rana Idan yatashi saiki dora tandarki awuta kizuba Mai idan yaizafi saiki rinka dibar kulunki kina zubawa.

Yadda ake sinasir din shinkafa

Abinci
SINASIR DIN SHINKAFA 3 cup Shinkafar tuwo1 cup Shinkafar ci2 tsp Baking powder2 tsp YeastSugar to your tasteOil HADAWA:Step 1Zaki jiga shinkafarki a ruwa da daddare kibarta takwana i mean the 2 both shinkafa Step 2Sai ki wanketa kizuba yeast a ciki sai ki kai markade Step 3Bayan kinkai markade tayi irin 3-4 hours ta tashi sai kisaka mata baking powder ki juya sannan kibarta takara tashi Step 4Sai kizuba sugar ki juya sai ki dan zuba ruwa kadan Step 5Kin dauko nonstick pan dinki sai ki shafa mai aciki sai ki fara suya aci dadi lapia

Yadda ake danwake

Abinci
YADDA AKE DANWAKE: 1/2 kwano garin alabo3 cup flour2 cup garin alkama1 cup garin kuka1 cup kanwa(Ajika da ruwa)Ruwa(iya adadin kaurin da ake bukata)Sinadaran hadawa(dandano)Yaji(iya adadin da akeso)Kwai(iya adadin da akeso)MaggiSoyayyen mai ko manja Dafarko kina bukatar garin alabo(rogo),alkama da kuma flour,ni hadasu nake dukka guri daya sai a nikomin su,idan an. Niko sai na tankade na zuba flour iya adadin danakeso,da kuka na yi mixing dinshi sosai, ABUN jan hankali,wanan adadin danasaka adadi ne mai yawa gaskiya sbda na cin mutane goma 12 ne da,amma kamar cimar mutum 2 sai ayi amfani da alabo kopi 1 flour rabin kopi,alkama ma rabin kopi. Dafarko bayan na tankade garina,na zuba garin kuka akai,na hadashi,sai na zuba jikakkiyar kanwa na akai Sai na zuba ruwa iya adadin da zai ...

Yadda ake dafa shinkafa jollof

Abinci
JOLLOF DIN SHINKAFA ME DADDAWA Shinkafa, jajjagen kayan miya Maggi, daddawa, mai Ruwa nama daddawa, mai YADDA AKE HADAWA Da farko zaki gyaran kayan miyanki,tumatir kadan,attarugu,tattasai,albasa,tafarnuwa,ki wanke ki nika/jajjaga Ki dora tukunyarki kan wuta,ki zuba mai,kisa yankakkar albasa idan yadanyi laushi kizuba tafasashen namanki,ki soya naman sama sama Idan yadayi ja,seki zuba jajjagen/nikakkun kayan miyanki,ki soya har su soyu,idan suka soyu ki zuba ruwan da ze iya dafa miki shinkafanki. Bayan kin zuba ruwan,ki zuba daddawanki dai dai yawan yanda kikeson kamshinta da gardinta ya fito miki a jolof dinki Kizuba maggi,da Dan gishiri kadan ki rufe har ruwan ya tafasa ki wanke shinkafarki ki zuba ki motsa sai ki rufe da mirfi Idan shinkafa...