Tuwon madara mai kwakwa
Yanda ake Tuwon Madara me kwakwa da butter.
Abubuwan da ake bukata:
Madara Loka 2:
Ruwa Karamin Kofi 3.
Sai Sugar Gwangwani 4.
Sai Butter Leda daya.
Sai Vanilla.
Robar Kwabi.
Kwanon Suya.
Muciya.
Farantin Silver.
Karamar wuka.
Da farko ana kankare kwakwa( wasu suna fara kankare bayan kwakwar su fitar dashi ya zama saura farin kwakwar kawai, wasu kuma basa kankarewa) se a sata a kasko a soya ba tare da an zuba mai ba, sama-sama za'a soya kada a bari tayi ja.
Se a sauke na a dora kason a sa ruwa karamin glass cup uku, ko kuma karamin kofin roba uku se a zuba sugar gwangwani hudu saboda madaran Loka biyu ce.
Da sugar din ya dahu yayi kauri Se a zuba kwakwan a ciki sannan a zuba butter a barshi ya dan kara dahuwa kadan.
A gefe guda kuma sai a samu...