Wednesday, January 15
Shadow

Amfanin Kwakwa

Yadda ake cincin din kwakwa

Amfanin Kwakwa
Don yin cincin din kwakwa, ga matakan da zaka bi: Abubuwan da ake bukata: Kwakwa guda 1 Zuma ko sikari Gishiri Man gyada ko man sunflower Kwano Fulawa Farin kwai (egg white) - idan kana so Ganyen kori ko cilantro don ƙamshi, idan ana so Matakan Hadawa: Fara da kwakwa: Fashe kwakwa ka zubar da ruwan kwakwar. Cire kwakwar daga cikin ƙwanson ta. Ki yayyanka kwakwar zuwa ƙananan pieces, sannan ki markade su a blender ko grinder har sai sun yi laushi, ko in ana iyawa a daka. Shirya Butter: A cikin kwano, haɗa markadadden kwakwa da fulawa. Sai a ƙara zuma ko sikari gwargwadon ɗanɗano. Idan kina so, ƙara farin kwai (egg white) don ya haɗa butter ɗin sosai. Ƙara ɗan gishiri. Idan kina son ƙarin ɗanɗano, zaki iya ƙara ganyen kori ...

Amfanin man kwakwa a gaban mace

Amfanin Kwakwa, Jima'i
Macen da gabanta bashi da ruwa ko baya kawo ruwa, yana bushewa, musamman a lokacin jima'i tana iya amfani da man kwakwa. Man kwakwa inji masaana yana hana bushewar gaban mace. Hakanan a wani kaulin, Man kwakwa yana sa hasken gaban mace. Ana shafashi shi kadai, ko kuma domin samun sakamako me kyau, a hada da ruwan lemun tsami a shafa, yana sa gaban mace yayi haske. Hakanan man kwakwa yana maganin kaikayin gaba dake damun mata ko kuma ace infection. Ana shafa man kwakwa a gaba dan magance yawan kaikai dake sa susa a ko da yaushe. Ana iya shafashi a saman gaban mace ko kuma a shafashi a cikin gaban, duk yana magani. Hakanan bincike ya nuna cewa,Man kwakwa na taimakawa mata masu fama da matsalar yoyon fitsari.

Amfanin man kwakwa a nono

Amfanin Kwakwa, Nono
Bincike ya tabbatar da man Kwa na maganin bushewa ko tsagewar kan nono. Ana shafa man kwakwa akan nono da yake bushewa ko ya tsage dan dawo dashi daidai. Hakanan idan kan nono yana zafi ko yana ciwo,shima bincike ya tabbatar da cewa, ana shafa man kwakwa kuma ana samun sauki da yardar Allah. Kuma idan kan nono yana kaikai, shima ana shafa man kwakwa dan magance wannan matsala. Hakanan wasu bayanai sun ce shafa man kwakwa akan nono yana batar da nankarwa da karawa nonon lafiya. Hakanan wasu bayanai sunce ana amfani da man kwakwa wajan sanya kan nono yayi haske, saidai bayanin yace sai an dauki lokaci kamar wata 2 ana shafawa kamin a samu sakamako me kyau. Hakanan wasu bayanai da ba'a tabbatar dasu ba sun ce shafa man kwakwa yana tayar da nonuwan da suka zube. Ana iya gwad...

Gyaran fuska da man kwakwa

Amfanin Kwakwa, Gyaran Fuska, Kwalliya
Man kwakwa na da amfani da yawa a fuska, yana sa fuska ta yi laushi, yana maganin ciwo yayi saurin warkewa, yana kuma taimakawa wajan rage kumburi. A wannan rubutun, zamu kawo muku amfanin man kwakwa wajan gyaran fuska. Wani bincike ya tabbatar da man kwakwa na taimakawa sosai wajan maganin kurajen fuska da kuma yana a matsayin rigakafi dake hana kurajen fitowa mutum a fuska. Hakanan man kwakwa na taimakawa wajan kawar da alamun tsufa a fuska. Ana shafa man kwakwa a fuska ko jiki kamar yanda akw shafa sauran mai. Hakanan ana cinshi da abinci.