Wednesday, January 15
Shadow

Duk Labarai

YANZU-YANZU: Kar ka jefa Kano cikin rikicin da ba za a iya gujewa ba, wasu Malaman Musulunci sun gargaɗi Gwamna Abba Kabir Yusuf

YANZU-YANZU: Kar ka jefa Kano cikin rikicin da ba za a iya gujewa ba, wasu Malaman Musulunci sun gargaɗi Gwamna Abba Kabir Yusuf

Duk Labarai, Kano
Malaman addinin Musulunci da Malaman addinin Musulunci a Jihar Kano, sun gargadi Gwamna Abba Yusuf da ya daina daukar duk wani mataki da zai jefa jihar cikin rikicin da ba za a iya kauce masa ba. Malaman da suka bayar da wannan shawara kan rikicin da ya barke a jihar, sun bayyana muhimmancin kaucewa yanke shawara da ka iya kawo cikas ga al’ummar jihar da kuma kara yiwa al’ummarta nauyi, wadanda tuni suka sha fama da munanan manufofin da suka gabata. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da Khalifa Sheikh Lawi Atiku Sanka, Khalifa Mal Abdulkadir Ramadan, Farfesa Abdulahi Pakistan, Malam Yusuf Ahmad Gabari, Lawan Abubakar Triumph, Sheikh Mohd Bakari, Imam Usaini Yakubu Rano, Imam Jamilu Abubakar da Farfesa Ibrahim Mabushira suka sanya wa hannu. Malaman addinin Islama...
Duk Abunda ya faru a Kano, Tinubu ne sila>>Inji Atiku

Duk Abunda ya faru a Kano, Tinubu ne sila>>Inji Atiku

Duk Labarai, Kano
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa idan yaki ya barke a Kano to shugaban kasa, Tinubu ne sila. Atiku ya bayyana cewa dalili kuwa shine Tinubu ya aika sojoji su je Kano su nada Sarki. Bayan da majalisar jihar Kano ta rushe duka sabbin masarautun da tsohon gwamnan jihar, Umar Ganduje ya kirkiro, an mayar da tsohon sarki, Muhammad Sanusi akan kujerar sarautar Kano inda aka tsige Aminu Ado Bayero. Saidai Aminu Ado Bayero bisa rakiyar sojoji wadanda ake kyautata zaton Gwamnatin tarayya ce ta bashi su ya koma Kano inda ya yada zango a karamar fadar sarki dake Nasara. Shi kuma sabon sarki, Muhammad Sanusi II yana can fada yana karbar mubaya'a daga hakimai da sauran mutanen gari. An dai zargi me baiwa shugaban kasa shawara, Nuhu Ribadu da hannu a...