Bama son A gina mana makarantu ko Tituna, A samar mana da tsaro kawai>>Inji Sanata Garba Musa Maidoki daga jihar Kebbi
Sanata Garba Musa Maidoki daga jihar Kebbi ya bayyana cewa, basa bukatar a samar musu da makarantu ko tituna a jiharsu.
Sanatan yace matsalar tsaro ta yi kamari a yankinsu ta yanda ya zu abinda kawai suke bukata shine tsaron ba wai a gina musu titi ko Makarantu ba.
Ya bayyana hakane yayin zaman majalisar.
https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1975918730048876615?t=qIRYNyO0HFO_a_SoI9HFxg&s=19








