Saturday, October 10
Shadow

Duk Labarai

Ka ku yi gaba da Dan uwanku ko me zai muku>>Inji Salma Bashir

Ka ku yi gaba da Dan uwanku ko me zai muku>>Inji Salma Bashir

Duk Labarai
Shahararriyar me sukar 'yan darika a kafafen sada zumunta, Salma ta bayyana cewa dan uwanta ya rasu. Tace amma abinda ya fi damunta shine ya rasu tana gaba dashi. Tace sun shaku sosai aka zo aka ce mata ya fadi wata magana. Tace bata tashi gaba dashi ba sai da ya kwanta ciwon Ajali. Tace ta shirya zata je su shirya aka ce mata ya rasu. Inda ta kara da cewa ba zata yafewa wadanda suka hadata dashi ba. https://www.tiktok.com/@salzee23/video/7693495600238611719?_r=1&_t=ZS-9ALjbgQK81t
Shaidun gani da Ido sun ce basu taba ganin abinda ya faruba a hadarin jirgin saman sojojin Najeriya

Shaidun gani da Ido sun ce basu taba ganin abinda ya faruba a hadarin jirgin saman sojojin Najeriya

Duk Labarai
A jiyane Jirgin saman Sojojin Najeriya NAF 931 yayi khadary da mutane 30 a cikinsa kuma duka babu wanda ya fita da rai. Hukumar sojojin saman ta tabbatar da faruwar lamarin. Lamarin ya farune a ilaje dake jihar Ondo. Shaidu sun bayyana cewa, sun yu hasashen direban jirgin yayi iya bakin kokarinsa dan kaucewa fadawa kan gidajen mutane inda ya samu ruwa ya fada. Saidai ba'a ga gawar ko mutum daya ba saidai kayan sawarsu, jirgin ma sai baraguzansa aka gani. Wasu shaidun sun ce kamar ruwan bude yayi jirgin ya fada cikinsa, ya koma ya kulle. Lamarin dai ya girgiza Al'ummar yankin sosai. https://twitter.com/citykush1/status/2107148538308145220
Zamu samarwa jihar Lagos wutar awanni 24>>Inji Gwamnatin Tarayya

Zamu samarwa jihar Lagos wutar awanni 24>>Inji Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa zasu samarwa Jihar Lagos wutar Lantarki ta awanni 24. Gwamnatin tace zasu Yi hadin gwiwa da jihar Lagos din wajan wannan aiki. Ministan wutar Lantarki, Joseph Tegbe ya bayyana hakan inda yace shirin bana jihar Lagos bane kadai amma zasu fara da jihar ne saboda itace ke da bukatar kaso 40 zuwa 50 na wutar Lantarkin Najeriya. Ya yiwa mazauna Lagos alkwarin Kwanannan zasu fara samun wutar awanni 24. Yace zasu fara da jihar Lagos ne amma idan shirin yayi nasara, zasu fadsashi zuwa sauran jihohin Najeriya. Tuni aka kafa kwamitin da zasu yi wannan aiki.
Kalli Bidiyon: Tsohon Shugaban kasar Nijar, Bazoum da ankwa a hannunsa zagaye da sojoji

Kalli Bidiyon: Tsohon Shugaban kasar Nijar, Bazoum da ankwa a hannunsa zagaye da sojoji

Duk Labarai
An hangi tsohon shugaban kasar Nijar, Muhammad Bazoum da ankwa a hannunsa zagaye da sojoji. An ga sojojin sun fito dashi daga wani gida inda yake murmushi. Sojoji sun hambarar da gwamnatin Bazoum inda suka dare kan karagar mulkin kasar, da zargin tsohon shugaban kasar da cin amanar kasa ta hanyar hada kai da kasar Faransa. https://twitter.com/musa_kiliya/status/2107214801537802489
Muna Zargin ‘Yan Izala sun boye Sheikh Lawal Triumph saboda tsoron Shari’a>>Inji Lauyan ‘yan Darika da suka kai Sheikh Lawal Triumph Kotu

Muna Zargin ‘Yan Izala sun boye Sheikh Lawal Triumph saboda tsoron Shari’a>>Inji Lauyan ‘yan Darika da suka kai Sheikh Lawal Triumph Kotu

Duk Labarai
Lauyan 'yan Darika da suka kai Sheikh Lawal Triumph kotu ya zargi cewa 'yan Izala sun Boye Sheikh Lawal Triumph. Ya kuma ce sun ga Alamar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf tsoron 'yan Izala yake saboda ya kasa daukar mataki akan Sheikh Lawal Triumph. Ya bayyana cewa Sheikh Lawal Triumph wannan ne karin farko kuma na karshe da zai yi irin wannan cin zarafi ga Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam). Ya bayyana hakane bayan zaman kotu na yau da aka yi game da shari'ar. https://www.tiktok.com/@itzhalifausaini/video/7693158822906498356?_r=1&_t=ZN-9AJA48DipaY A bangaren Lauya me kare Sheikh Lawal Triumph yayi zargin cewa 'yan darika sun je da mutane kotun dan su tayar da hankali. https://www.tiktok.com/@taskarmalanlawantriumph/video/7693148810880716053?_r=1&_t=ZN-9AJAmDS...
Kalli Bidiyon: Gfresh Al-amin yayi magana kan rahoton dake cewa ya saki Sadiya Haruna a Saudiyya

Kalli Bidiyon: Gfresh Al-amin yayi magana kan rahoton dake cewa ya saki Sadiya Haruna a Saudiyya

Duk Labarai
A yau da safe mun tashi da rahoton dake cewa, Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya saki matarsa a kasar Saudiyya. Gfresh Da Sadiya dai suna kasar Saudiyya inda suke aikin Umrah. Rahoton yace wai Sadiya Haruna ta kama Gfresh ne yana waya da tsohuwar matarsa, Maryam Nicki Minaj abinda ya hadasu fada kenan har ya saketa. Saidai a martaninsa, Gfresh Al-amin ya musanta wannan Rahotan inda yace bai saki Sadiya ba https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7693190029337758984?_r=1&_t=ZN-9AIxuWDZggA