Daga yanzu zuwa kowanne lokaci, Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, zai mika takardar murabus dinsa, in dai ba canja ra'ayi ya yi ba.
Majiyoyi sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa za a maye gurbin Ganduje da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na ƙasa na yanzu har zuwa lokacin babban taron jam’iyyar da za a yi a watan Disamba.
Rahotanni sun nuna cewa wannan mataki na murabus na da nufin shawo kan korafe-korafe daga jiga-jigan jam’iyyar daga yankin Arewa ta Tsakiya, da kuma ƙara karfin tasirin muryar adawa daga cikin jam’iyyar da ke ƙara ta’azzara.
Idan za a iya tunawa an nada Ganduje a watan Agusta 2023 bayan murabus din Abdullahi Adamu daga wannan mukami.
Tun daga lokacin, jiga-jigan siyasa daga Arewa ta Tsakiya suna ci gaba da neman a mayar da kujerar shugabancin jam’iyy...
Rahotanni sun bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai mayar da Gwamna Simi Fubara na jihar Rivers kan mukaminsa na gwamnan jihar.
Saidai an gindayawa gwamnan Sharuda kamar haka:
Ba zai sake tsayawa takarar gwamnan ba a zaben shekarar 2027.
Zai yadda Wike ya tsayar da 'yan takarar shuwagabannin kananan hukumomi 23 dake fadin jihar.
Hakanan ya yadda ya biya 'yan majalisar jihar dakewa Wike Biyanna su 27 hakkokinsu da ya dakatar, idan ya yadda da hakan, 'yan majalisar ba zasu yi yunkurin tsigeshi ba.
Wata mamakon gobara ta barkena tsakiyar kasar Israyla inda take ta yaduwa sosai.
Gobarar da ba'a san inda ta samo Asali ba ta tashine a birnin Ness Ziona kuma 'yan kwana-kwana na ta kokarin kasheta.
Rahotanni sun ce an tattaro ma'aikatan kwana-kwana daga yankuna daban-daban dan su taimaka a kashe gobarar.
Hukumomi sun ce Tuni aka fara kwashe mutane daga gidajen da Gobarar ta durfafa.
Wannan Bidiyon yanda fada ya kaurene tsakanin wani dan Karota da me adaidaita sahu.
An ga yanda me Adaidaita din ya daga dan karotan ya narka da kasa. Saidai daga baya an rabasu.
kalli Bidiyon anaan
Dattijon Arziki, Sheikh Dahiru Bauchi Ya Cika Shekara 101 A Duniya.
….Yana da ’ya’ya kimanin 100 da jikoki 406, da tattaba-kunne 100, wadanda su ma suka gaje shi a fannin haddar Kur’ani
Daga Ishaq Ismail Musa
An haifi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ne a ranar 2 ga watan Muharram a shekara ta 1346 bayan hijira, inda a gobe Juma’a, 2 ga Muharram na shekarar 1447, yake cika shekaru 101 cif a ban kasa.
Duk da cewa iyalai da almajiran Maulana Shehu Dahiru Usman Bauchi ba su yi wani biki don taya shi murnar cika shekara 100 a duniya, amma masoya da almajiran Shehin Malamin sun bayyana farin cikinsu da yi masa addu’o’i musamman a dandali daban-daban na shafukan Intanet.
Sun yaba da irin hidimar da ya yi wa Musulunci da Bil Adama, inda suka jinjina rawar da ya taka a matsayinsa na s...
Ina Mai Godewa Allah Da Ba Na Cikin Wadanda Za A Tambaya Kan Wannan Màsifàr Da Gwamnatin Tinubu Ta Jefa Al'ummar Nijeriya A Ciiki, Cewar El-Rufa'i
A bin tambaya shine, a gobe ķiyamà Elrufai yake nufi ko a nan gidan duniya?
Malaman Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar Kaduna watau Nuhu Bamalli Polytechnic, Zaria sun koka da karancin Albashi inda suka ce matasa masu bautar kasa sun fi su daukar albashi me kyau.
Hakanan malaman Kwalejin ilimi ta jihar, College of Education, Gidan Waya suma sun koka akan irin wannan lamari.
Jaridar Punchng ta ruwaito cewa, malaman Makarantar na daukar albashin 63,000 zuwa 65,000. A yayin da su kuma matasa masu bautar kasa ake biyansu Naira 77,000 duk wata.
Malam sun ce wannan cin fuska ne kuma ta yaya mutum mai iyali zai iya gudanar da rayuwarsa da Albashin Naira 65,000 a wata?
Rahoton yace malaman zun zargi cewa hakan nuna halin ko in kula ne a bangaren ili a jihar, wasu daga cikin malaman dai na da kwarewa ta shekaru 10.
Rahoton yace wannan dalili yasa malamai su...
Sabbin hotunan Tauraruwar fina-finan Hausa, A'isha Saleh sun tayar da kura a kafafen sada zumunta inda aka ganta cikin wata shiga dake nuna surar jikinta.
A yayin da wasu suka yaba, wasu sun ce shigar bata dace da ita ba.
Wasu na tambayar shin wai musulmace inda wasu ke cewa ko dai ta bar musuluncinne?