Friday, December 19
Shadow

Duk Labarai

Sai watan Janairun 2026 sabbin dokokin haraji za su fara aiki – Gwamnatin Najeriya

Sai watan Janairun 2026 sabbin dokokin haraji za su fara aiki – Gwamnatin Najeriya

Duk Labarai
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ba za ta fara aiwatar da sababbin dokokin haraji da Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu ba sai a watan Janairun 2026. Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan bikin saka wa dokokin huɗu hannu a yau Laraba, shugaban kwamatinn hukumar tattara harajin Zach Adedeji ya ce za su kammala tsara komai kafin lokacin aiwatar da su. Ya ƙara da cewa za su yi amfani da tazarar wata shidan wajen bai wa waɗanda ke da alhakin aiwatar da dokar damar shiryawa da kuma tabbatar da cewa an wayar da kan dukkan 'yan Najeriya game da dokokin. Ya tabbatar da cewa saka wa dokokin hannu ya sauya sunan ma'aikatarsa daga Federal Inland Revenue Service (FIRS) zuwa Nigeria Revenue Service.
Hukumar zabe me zaman Kanta, INEC zata ci gaba da yiwa ‘yan Najeriya rijistar katin zabe

Hukumar zabe me zaman Kanta, INEC zata ci gaba da yiwa ‘yan Najeriya rijistar katin zabe

Duk Labarai
Hukumar zabe me zaman kanta tace zata ci gaba da rijistar masu zabe a ranar 17 ga watan Yuli a jihar Anambra inda kuma za'a ci gaba da yi a gaba dayan Najeriya a ranar 18 ga watan Augusta. Shugaban hukumar, Prof. Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a wajan wani taro da aka yi ranar Alhamis a Abuja. Ya bayyana cewa, za'a fara rijistar ne a jihar Anambra saboda zaben gwamna da za'a gudanar a jihar.
Sharrine aka kalamin ban baiwa dana manyan filaye a Abuja ba>>Inji Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike

Sharrine aka kalamin ban baiwa dana manyan filaye a Abuja ba>>Inji Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa babu gaskiya a maganar da ake yadawa wai ya baiwa dansa filaye a manyan unguwannin Abuja. Me magana da yawun ministan, Lere Olayinkane ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar ga manema labarai inda yace ko fili daya Wike be baiwa dansa ba. A baya dai hutudole ya kawo muku rahoton dake cewa kafar Peoplesgazette ta ce ta samu bayanan sirri cewa, Wike ya rabawa 'ya'yansa filaye a Abuja. Saidai Wike yace wannan magana karyace da ta fito daga bakin 'yan jaridar da basu da kwarewa a aikinsu. Wike yace a ina za'a samu filaye da yawa a Asokoro da Maitama wanda har zai rabawa 'ya'yansa? Yace idan kuma jaridar tace gaskiyane rahoton data wallafa to ta kawo takarda me dauke da sunan dan Wike dake nuna alamar cewa ya mall...
Ji yanda Naira Tiriliyan 210 ta yi batan dabo a kamfanin mai na kasa, NNPCL

Ji yanda Naira Tiriliyan 210 ta yi batan dabo a kamfanin mai na kasa, NNPCL

Duk Labarai
Rahotanni daga majalisar tarayya na cewa binciken yanda kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya gudanar da ayyukansa yasa an gano naira Tiriliyan 210 da suka bace. Dan haka kwamitin dake kula da asusun ajiyar kudaden gwamnati na majalisar tarayya ya baiwa kamfanin na NNPCL kwanaki 10 ya bayar da ba'asi kan yanda aka yi da kudin. Shugaban kwamitin, Senator Aliyu Wadada, SDP daga jihar Nasarawa ne ya bayyana hakan inda yace kamfanin na NNPCL ya nemi a bashi watanni 2 dan ya tattaro bayanai game da lamarin amma sun ki amincewa inda suka ce sun basu kwanaki 10. Yace idan kuma basu bayar da bayanan da ake bukata ba to lallai za'a dauki mataki me tsauri akan su.
Kalli Jadawalin shafukan da ‘yan Najeriya suka fi ziyarta a wajan Mayu da ya gabata

Kalli Jadawalin shafukan da ‘yan Najeriya suka fi ziyarta a wajan Mayu da ya gabata

Duk Labarai
Wadannan sune shafukan da 'yan Najeriya suka fi ziyarta a watan Mayu da ya gabata. 1 Bet9Ja — 32.89m2 Nkiri — 18.47m3 Betking — 11.89m4 Nairaland — 10.83m5 Nigerianpasc — 8.74m6 Legit — 6.11m7 Jamb — 5.75m8 Jiji — 4.56m9 Punchng — 4.5m10 9Jarocks — 4.43m11 Trendybeatz — 4.43m12 Nysc — 3.27m13 Vanguardngr — 3.25m14 Darknaija — 3.13m15 Paystack — 2.27m
Kungiyar dattawan Yarbawa ta Afenifere ta yi kira ga shugaba Tinubu da ya gaggauta amincewa da kafa ‘yansandan Jihohi

Kungiyar dattawan Yarbawa ta Afenifere ta yi kira ga shugaba Tinubu da ya gaggauta amincewa da kafa ‘yansandan Jihohi

Duk Labarai
Kungiyar dattawan Yarbawa ta Afenifere ta yi kira ga shugaba kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya gaggauta amincewa da kafa 'yansandan jihohi. Kungiyar ta bayyana hakane bayan taro na masu ruwa da tsaki da ta yi a gidan shugabanta, Chief Reuben Fasoranti dake Akure. Ta yi kira ga shugaban kasar da ya fitar da kudirin doka wanda zai bayar da damar canja kundin tsarin mulkin Najeriya dan a samar da 'yansandan Jihohi inda tace ya aika da wannan kudirin dokar zuwa majalisa. Hakan na kunshene a cikin sanarwar da sakataren yada labaran Kungiyar, Jare Ajayiya fitar inda yace sun yaba da kokarin Gwamnati na magance matsalar tsaro amma akwai bukatar a kara himma.
Ba a cire Atiku a matsayin Wazirin Adamawa ba — Gwamnatin Adamawa

Ba a cire Atiku a matsayin Wazirin Adamawa ba — Gwamnatin Adamawa

Duk Labarai
Ba a cire Atiku a matsayin Wazirin Adamawa ba — Gwamnatin Adamawa. Gwamnatin Jihar Adamawa ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen yada labarai cewa ta cire tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, daga sarautar Wazirin Adamawa. A baya-bayan nan, gwamnatin jihar ta fitar da wata sanarwa da ke bayyana cewa mutanen da ke masarautar su ne kaɗai ke da hakkin naɗa basarake da mambobin majalisar masarauta. Wannan sabon tsarin ya sa kafafen yada labarai da dama suka fassara cewa an cire Atiku daga matsayin Wazirin Adamawa. Amma a wani taron manema labarai da aka gudanar a jiya Laraba, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare na Jihar Adamawa, Iliya James, ya bayyana cewa wannan sabon tsarin bai cire kowa daga mukaminsa ba. Ya kuma ƙara da cewa duk wasu sabbin shirye-s...
2027: Idan Tinubu ya bani takarar mataimakin shugaban ƙasa da gudu zan karɓa – Barau Jibrin

2027: Idan Tinubu ya bani takarar mataimakin shugaban ƙasa da gudu zan karɓa – Barau Jibrin

Duk Labarai
2027: Idan Tinubu ya bani takarar mataimakin shugaban ƙasa da gudu zan karɓa - Barau Jibrin. Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana cewa ko da yake ba ya son ya shiga cikin muhawarar wanda zai iya zama abokin takarar Shugaba Bola Tinubu a 2027, zai karɓi kowane nau’in aiki da Shugaban ƙasa zai danka masa cikin farin ciki da biyayya. Yayin wani taron manema labarai da aka shirya dangane da shirin jin ra’ayoyin jama’a a shiyyoyi daban-daban da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sauya Kundin Tsarin Mulki , Barau ya ce: “Duk abin da Shugaba ya bukace ni da in yi, zan yi shi dari bisa dari ” Wannan bayani na zuwa ne bayan wata magana da ya yi a ranar Talata, inda ya shawarci wata ƙungiya da ke goyon bayan kudurin sa ya zama mataimakin shugaban kasa a 202...