Babu Inda Na Ce Sai Mun Bada Cin Hancin Milyan Uku Kafin A Ba Mu Damar Gabatar Da Kudiri A Majalisar Tarayya, Cewar Hon Usman Ibrahim Auyo
Babu Inda Na Ce Sai Mun Bada Cin Hancin Milyan Uku Kafin A Ba Mu Damar Gabatar Da Kudiri A Majalisar Tarayya, Cewar Hon Usman Ibrahim Auyo
Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Hadejia, Auyo da Kafin Hausa dake jihar Jigawa, Honarabul Usman Ibrahim Auyo, wanda ake yi wa lakabi da Kamfani ya nesanta kansa da labarin karya da aka yada akansa, wanda aka ce ya ce ba a ba su damar gabatar da kudiri a majalisa har sai sun bada cin hancin naira milyan uku ko fiye da haka. Sannan kuma sai sun yi ta kamun kafa ga sauran 'yan majalisun.
A cewarsa ba ya na nufin majalisa ake baiwa wannan kudin ba, a duk sanda mutum zai gabatar da kudiri, akwai wadanda daga waje aikin su shine ka ba su kwangilar rubuta maka kudiri ka biya su, kafin daga bisani ka nemi shawarwari daga wajen takwaro...







