In da na ci zaɓe nima sai na cire tallafin man fetur amma ba farar-ɗaya irin na Tinubu ba>>Obi
In da na ci zaɓe nima sai na cire tallafin man fetur amma ba farar-ɗaya irin na Tinubu ba - Obi
Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, ya ce da ya ci zaɓen da shi ma sai ya cire tallafin man fetur kuma ya kyale Naira ta neman wa kan ta daraja, kamar sai yadda shugaba Bola Tinubu ya yi.
Da ya ke magana a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise a jiya Litinin, Obi ya ce da zai aiwatar da manufofin a hankali a hankali ba farar-ɗaya ba gaba-gaɗi irin na Tinubu ba.
Tsohon gwamnan na Anambra ya ce kowa ya san cewa dole ne a kawo karshen "baƙala da cin hanci da rashawa" da ke tattare da tsarin tallafin man fetur.
Obi ya yi tambaya kan inda kudaden da ake tarawa cire daga tallafin man fetur suke tun lokacin da aka cire shi, ya kara d...








