Ba wanda yake da hujja kan mijina (Abacha) ya saci kuɗin Najeriya, kuma bai soke zaɓen Abiola ba – in ji Maryam Abacha
Uwargidan marigayi tsohon shugaban Najeriya, Maryam Abacha, ta musanta zargin da ake yi wa mijinta, tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji, Janar Sani Abacha, kan zargin satar kuɗin Najeriya.
Abacha ya yi mulkin Najeriya ne daga shekarar 1993 zuwa 1998 kuma ya rasu ne a ranar 8 ga Yunin 1998.
DailyTrust ta rawaito a cikin wata hira da gidan talabijin ɗin TVC ya yi ta yi a ranar Lahadi kan cikar Abacha shekaru 27 da rasuwa, uwargidan marigayin ta ce kuɗin da ake zargin mijinta ya sata, ba satar su ya yi ba, kawai ana yi masa mummunar fassara ce.
A cikin waɗannan shekarun baya-bayan nan, gwamnatoci daban-daban sun sanar da gano miliyoyin kuɗin dalar Amurka a asusan ƙasashen waje waɗanda ake wa laƙabi da “Abacha loot.”
Waɗannan kuɗaɗe, an dawo da su daga ƙasashen Switzerland da Amurk...








