Gwamnonin Zamfara da Benue sun ƙalubalanci gayyatar kwamitin majalisar wakilai
Gwamnonin jihohin Zamfara da Benue, Dauda Lawal da Hyacinth Alia, sun ƙi amincewa da gayyatar da Kwamitin Karɓar Ƙorafe-ƙorafe na Majalisar Wakilai ta Tarayya ya aike musu, inda suka bayyana shakku kan halaccin gayyatar.
An gayyaci gwamnonin da majalisun dokokin jihohinsu ne domin su bayyana a gaban kwamitin bisa zargin karya ƙundin tsarin mulki da kuma gazawa wajen gudanar da mulki.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai na kwamitin, Chooks Oko, ya fitar
Sanarwar ta bayyana cewa an tsara zaman sauraron bayanansu ne a ranar 8 ga watan Maris, inda ake sa ran za su bayar da ƙarin haske kan wasu muhimman al’amura.
Daga cikin matsalolin da ake son jin bayani a kansu har da dakatar da wasu 'yan majalisar jiha da kuma taɓarɓarewar tsaro a jihohin biy...








