Kotu ta kori ƙarar da aka kai Buhari da Emefiele kan sauya fasalin takardar Naira
Kotu ta kori ƙarar da aka kai Buhari da Emefiele kan sauya fasalin takardar Naira
A jiya Litinin ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kori karar da aka shigar kan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ana neman fansar Naira biliyan 1 kan wahalhalun da tsarin sake fasalin Naira na 2023 ya haifar.
Mai shari’a Inyang Ekwo ne ya yi watsi da karar bisa hujjar cewa wanda ya shigar da karar bai maida hankali kan shari'ar ba.
Wani lauyan mazaunin Abuja, Uthman Tochukwu SAN ne ya shigar da karar, wanda ya zargi wadanda ake ƙarar da jefa ƴan Najeriya cikin wahala mai tsanani ta hanyar wannan shiri na sake fasalin Naira.
Karar, mai lamba FHC/ABJ/CS/418/2023, ta haɗa da Buhari da babban lauyan gwamnatin tarayya, da kuma tsoho...








