Sunday, December 21
Shadow

Duk Labarai

IMF ta baiwa Gwamnatin Tinubu shawarar ta kara kaimi wajan karbar Haraji

IMF ta baiwa Gwamnatin Tinubu shawarar ta kara kaimi wajan karbar Haraji

Duk Labarai
Kungiyar bada Lamuni ta Duniya, IMF ta baiwa Gwamnatin tarayya shawarar cewa su kara kaimi wajan karbar haraji. Wakiliyar kungiyar, Kristalina Georgieva ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar a birnin Washington DC. Ta bayyana cewa, ya kamata gwamnatin ta yi amfani da fasahar zamani wajan karbar harajin. Ta bayyana cewa, bayar da shawara irin wannan ya zama dole musamman lura da cewa farashin man fetur da Najeriya ta dogara dashi wajan samun kudin shiga ya fadi a kasuwannin Duniya.
Karya ake mana bamu biya Biliyan 6 ba na diyyar mafarautan Kano da aka kònà>>Inji Gwamnatin jihar Edo

Karya ake mana bamu biya Biliyan 6 ba na diyyar mafarautan Kano da aka kònà>>Inji Gwamnatin jihar Edo

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Edo ta musanta ikirarin kungiyar IPOB dake cewa ta biya Biliyan 6 a matsayin diyyar mafarauta 16 da aka kashe aka Kona a jihar. Kakakin Gwamnatin jihar, Fred Itua yace maganar kungiyar IPOB ba ba gaskiya bace, basu bayar da naira Biliyan 6 a matsayin kudin diyyar kisan wadannan mafarauta da aka kona ba. Yace maganar ta IPOB kawai sun yi tane dan kawo hargitsi da gwara kawunan mutane. Dan haka ya bukaci mutane su yi watsi da wannan magana.
Ji alkawarin da aka yiwa ‘Yan majalisar NNPP da suka koma APC

Ji alkawarin da aka yiwa ‘Yan majalisar NNPP da suka koma APC

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan majalisar jam'iyyar NNPP da suka koma jam'iyyar APC an musu alkawari me tsoka. Daga cikin Alkawuran da aka musu akwai maganar cewa, kowanne dan majalisa zai koma kan kujerarsa ba tare da an tsayar da kowa ba yayi takara dashi. Wata majiya daga jam'iyyar NNPP dince ta bayyana hakan. A jiyane dai Shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya karbi wasu 'yan jam'iyyar ta NNPP da suka koma cikinta.
Kalli Hotuna: An Kama Hanyar Zuwa Daurin Auren Mawaki Rarara Da Aisha Humaira A Garin Maiduguri

Kalli Hotuna: An Kama Hanyar Zuwa Daurin Auren Mawaki Rarara Da Aisha Humaira A Garin Maiduguri

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} An Kama Hanyar Zuwa Daurin Auren Mawaki Rarara Da Aisha Humaira A Garin Maiduguri.
Ko a jikina, Ban ma san ana yi ba>>Inji Atiku game da komawar mataimakin sa Okowa da wasu jam’iyyar APC

Ko a jikina, Ban ma san ana yi ba>>Inji Atiku game da komawar mataimakin sa Okowa da wasu jam’iyyar APC

Duk Labarai
Tawagar tafiyar Atiku Abubakar ta mayar da martani kan maganar komawar wasu 'yan jam'iyyar PDP zuwa APC ciki hadda mataimakinsa Ifeanyo Okowa a zaben 2023 da kuma Gwamnan jihar Delta Rt. Hon. (Elder) Sheriff Francis Orohwedor Oborevwori. Tawagar tace sam hakan bai damesu ba kuma be dauke musu hankali ba a kokarin da suke na kwace mulki daga hannun Tinubu ba a shekarar 2027. Me magana da yawun tafiyar ta Atiku, Salihu Moh. Lukman ne ya bayyana hakan inda yace dama hakan bai zo musu da mamaki dan sun sam dama akwai wadanda kewa Tinubu aiki a cikin jam'iyyar tasu. Yace nan gaba ma akwai yiyuwar wasu karin Gwamnonin zasu koma APC. Saidai yace Dimokradiyya kenan, dama ita tana kafuwane a kan gasa. Yace hakan ba zai dauke musu hankali kan abinda suke na kokarin kafa tafiyar hadak...
Babban Hafsan Sojin Ƙasa ya bai wa dakarunsa wa’adin wata guda su kawar da ‘yan bìndìgà

Babban Hafsan Sojin Ƙasa ya bai wa dakarunsa wa’adin wata guda su kawar da ‘yan bìndìgà

Duk Labarai
Babban Hafsan Sojin Ƙasa ya bai wa dakarunsa wa’adin wata guda su kawar da ‘yan bindiga a Kwara. Shugaban rundunar sojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya bai wa sojoji umarnin su kawar da ‘yan bindiga daga Jihar Kwara cikin wa’adin wata guda. Oluyede ya bayar da wannan umarni ne yayin da yake jawabi ga dakarun da ke barikin Sobi a Ilorin, babban birnin jihar. Ya umarce su da su kawar da ‘yan bindigar daga ƙananan hukumomi biyu, yana mai jaddada cewa yana so a kammala aikin cikin wata guda. Shugaban sojojin ya ce Najeriya ba za ta iya yarda ‘yan bindiga su sake bazuwa zuwa wani yanki na ƙasar ba. Ya ƙara da cewa, ba za a yarda a samu wani irin taɓarɓarewar tsaro irin na Boko Haram a ko’ina cikin ƙasar ba. Oluyede ya ce, “Don haka, kuna nan kuma na san za ku iya...
Kalli Hotuna: Mun cinye zaben shekarar 2027 mun gama>>Inji Ganduje Bayan da ya karbi ‘yan NNPP da suka koma APC

Kalli Hotuna: Mun cinye zaben shekarar 2027 mun gama>>Inji Ganduje Bayan da ya karbi ‘yan NNPP da suka koma APC

Duk Labarai
Shugaban jam'iyyar APC na Kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje ya karbi jiga-jigan jam'iyyar NNPP wadanda su ka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC. Mashawarci na musamman ga Dr. Ganduje, Aminu Dahiru ne ya wallafa hotunan yadda tarbar ta kasance. Ganduje bayan karbar sabbin 'yan APC din ya bayyana cewa sun lashe zaben shekarar 2027 sun gama. Ya bayyana cewa akwai karin Gwamnoni da manyan 'yan siyasa da zasu shiga jam'iyyar tasu. Daga cikin wadanda Abdullahi Umar Ganduje ya karba sun hada da Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila da dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Rano/Kibiya/Bunkure, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum da tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano Dr. Baffa Bichi da tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Danbatta...
Bankin Duniya ya nada Dangote babban Mukami

Bankin Duniya ya nada Dangote babban Mukami

Duk Labarai
Babban Bankin Duniya (World Bank) ya nada Aliko Dangote tare da wasu manyan ‘yan kasuwa da masana daga sassa daban-daban na duniya zuwa mukamai na musamman a wani sabon kwamiti da aka kafa domin karfafa ci gaban tattalin arziki da rage talauci. An bayyana cewa wannan nadin na nuna yadda Bankin Duniya ke daraja ƙoƙarin da Dangote ke yi wajen bunkasa masana’antu da kuma tallafa wa ci gaban al’umma musamman a nahiyar Afirka. Baya ga Dangote, akwai wasu fitattun mutane da suka haɗa da shugabannin kamfanoni, masana tattalin arziki, da wakilan ƙungiyoyin kasa da kasa da za su yi aiki tare da bankin domin samar da hanyoyin warware matsalolin da ke hana ci gaba a duniya. Wannan ci gaba na daga cikin shirin Bankin Duniya na samar da tsayayyen tsarin ci gaba mai dorewa da kuma jawo hankalin...
Hoto: ‘Yan Bìndìgà sun kàshè Ango sun gudu da Amaryarsa

Hoto: ‘Yan Bìndìgà sun kàshè Ango sun gudu da Amaryarsa

Duk Labarai
' Yan Bindiga a garin Akaleku village dake karamar hukumar Obi ta jihar Nasarawa sun kashe wani Ango inda suka yi garkuwa da Amaryarsa. Harin ya saka fargaba a tsakanin mutane sosai. Maharan sun kai harinne ranar Laraba da misalin karfe 11 na dare. Sun kashe Angon me suna Alu Anzaku wanda aka daurawa aure ranar 12 ga watan Afrilu. Zuwa yanzu dai babu wata magana daga bakin jami'an tsaro game da lamarin.