Za a samar da ƙarin kayan aiki don daƙile ƴan ta da ƙayar-baya – Janar Chris Musa
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa sojoji na aiki tukuru domin shawo kan matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a baya-bayan nan.
Ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin samar da ƙarin kayan aiki - musamman na sama domin ƙarfafa yaƙi da ƴan ta da ƙayar baya da ake yi.
Janar Musa ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da shugaban Najeriyar ya yi da manyan hafsoshin tsaron ƙasar a fadarsa da ke Abuja ranar Juma'a.
Babban hafsan ya ƙara da cewa tuni aka sayo kayan yaƙin domin daƙile ayyukan masu iƙirarin jihadi, waɗanda suka zafafa kai hare-hare a ƴan watannin nan, musammman a yankin arewa maso gabashin ƙasar.
"Shugaban ƙasa ya ba da umarnin abu na gaba da za a yi, da kuma haɗa-kai da sauran ƙasashe da muke makwabtaka da su ...








