Kalli Bidiyo: Iyayen mu da suka rika haihuwar ‘ya’ya talatin akwai saukin rayuwa a lokacin amma yanzu Rayuwa ta canja dole mutum ya kula da yawan ‘ya’yan da zai haifa>>Sheikh Ibrahim Maqari
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Ibrahim Maqari ya jawo hankalin mutane akan tara 'ya'ya.
Yace a baya mutane na haihuwar 'ya'ya talatin saboda akwai wadatar gurin zama kuma a wancan lokacin ba sai an saka yaro a makaranta ba.
Yace amma yanzu Rayuwa ta canja, irin wancan abin ba zai yiyu ba.
https://www.tiktok.com/@prof.ibrahim.maqa92/video/7500248373430078725?_t=ZM-8wB1sZ5f0AZ&_r=1
Saidai malam yace irin mutanen mu na da wahalar canjawa akan wani abu da suka saba dashi.








