APC ta Kano ta yi kira da a kama Kwankwaso
APC ta Kano ta yi kira da a kama Kwankwaso
Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta bukaci a kama jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma dan takarar Shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
A wata Sanarwa da Abdullahi Abbas Shugaban APC a Kano ya fitar, jam’iyyar ta zargi Kwankwaso da yin zarge-zarge marasa tushe ga Gwamnatin Tarayya.
Dimokuradiyya TV ta ruwaito cewa, a yayin bikin kaddamar da aikin gina Titi mai tsawon kilomita 85 a garin Madobi, Kwankwaso ya ce Gwamnatin APC karkashin jagoranci Gwamnatin Tarayya na yunkurin kawo cikas ga zaman lafiya a Kano.
Amma Abbas yace ba wata barazana da Kwankwaso zai iya yi wa Gwamnatin Tarayya.
Muna so mu yi kira ga jami’an tsaro da kakkausar murya da su kamo Kwankwaso, domin ya tona asirin wadanda ya kira makiyan Jihar Ka...








