Friday, July 10
Shadow

Duk Labarai

Ji yanda Dansandan Najeriya ya bide wuta a ofishin ‘yansandan ya ķķàshè mutum daya ya kuma jikkata wasu

Ji yanda Dansandan Najeriya ya bide wuta a ofishin ‘yansandan ya ķķàshè mutum daya ya kuma jikkata wasu

Duk Labarai
Dansandan Najeriya me suna Effiong Bassey ya bude wuta a Ofishin da yake aiki na Atakpa Divisional Police dake jihar Cross Rivers inda ya kashe wata mata daya sannan ya jikkata wasu mutane 2. Lamarin ya farune da dukudukun ranar Lahadi bayan da Effiong ya koma ofis bayan ya kammala aikin dare a bankin Ekondo Microfinance Bank. Kakakin 'yansandan jihar, Ugbo Irene ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace Effiong ya nuna rashin da'a inda aka bukaci ya bayar da bindigarsa ta AK47 amma yaki. Yace ya tare kofar shiga ofishin inda ya hana shiga ko fita kamin daga baya ya bude wuta. Yace cikin mutane masu wucewa da ya harba hadda wata mata me suna Ijeoma Wilson Obot 'yar kimanin shekaru 41 da haihuwa wadda ta rasu, sauran 2 kuma suka jikkata. Yace tuni kwararrun 'yansanda suka je w...
HOTUNA DA ƊUMI-ƊUMI: KALLI YANDA ‘Yáɲ Gombe Sun Daka Wawa Ga Shinkafar Seyi Tinubu

HOTUNA DA ƊUMI-ƊUMI: KALLI YANDA ‘Yáɲ Gombe Sun Daka Wawa Ga Shinkafar Seyi Tinubu

Duk Labarai
Wasu matasa a jihar Gombe sun daka wawa kan shinkafar Seyi Tinubu. Ance motar ce ta yi faci ta tsaya sai kuma aka ankara cewa tallafin abincin Seyi Tinubu ne cike a motar, daga nan ne aka hau warwaso babu ji babu gani. Ana raɗe-raɗin cewa Seyi ya haƙura da zuwa sauran jihohin Arewa ne duba da yadda ake ta ƙorafi kan abincin da yake rabawa al'ummar Arewa. Me zaku ce?
Ya kamata a rikawa ‘yan Majalisar mu ta dattijai Gwajin shan miyagun kwàyòyì>>Sanata Natasha Akpoti ta bada shawara

Ya kamata a rikawa ‘yan Majalisar mu ta dattijai Gwajin shan miyagun kwàyòyì>>Sanata Natasha Akpoti ta bada shawara

Duk Labarai
Sanata Natasha Akpoti ta bayar da shawarar cewa, ya kamata a rika wa 'yan majalisar Dattijai gwajin shan miyagun kwayoyi. Ta bayyana hakane a matsayin martani ga sanata Sunday Karimi wanda shima dan jihar ta Kogi ne inda ya fito yana sukarta kan fadanta da sanata Godswill Akpabio. Yace Natasha Akpoti ta jawowa jiharsu ta Kogi abin kunya sannan ta jawowa Najeriya ma abin kunya saboda abinda ta yi. Yace fadan da sanata Natasha Akpoti ta yi da Godswill Akpabio ya nuna cewa, tsohon Gwamnansu na da gaskiya akan fadan da suka yi da sanata Natasha Akpoti. A baya dai, tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello sun sha dambarwa da Sanata Natasha Akpoti. Sanata Sunday yace sun yi kokarin baiwa Sanata Natasha Akpoti baki amma taki fahintarsu.
Adamu Abdullahi Kenan, Wanda Ya Kare Da Sakamako Mafi Kyau A Jami’ar Tarayya Dake Gashua A Jihar Yobe

Adamu Abdullahi Kenan, Wanda Ya Kare Da Sakamako Mafi Kyau A Jami’ar Tarayya Dake Gashua A Jihar Yobe

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Adamu Abdullahi Kenan, Wanda Ya Kare Da Sakamako Mafi Kyau A Jami'ar Tarayya Dake Gashua A Jihar Yobe Wace fata za ku yi masa?
Sheikh Kabiru Gombe Ya Tara Wa Marayu Zunzurutun Kuɗi Har Naira Miliyan 67

Sheikh Kabiru Gombe Ya Tara Wa Marayu Zunzurutun Kuɗi Har Naira Miliyan 67

Duk Labarai
Sheikh Kabiru Gombe Ya Tara Wa Marayu Zunzurutun Kuɗi Har Naira Miliyan 67. {"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Sheikh Muhammad Kabir Gombe, Ya Tara Wa Marayu Zunzurutun Kuɗi Har Naira Miliyan 67 Inda Ya Ke Karatun Tafsirin Al-Quran Maigirma, Cikin Wannan Watan Azumin Ramadana A Masallacin Helkwatar Ƙungiyar Izala Dake Unguwar Utako, Birnin Tarayya, Abuja, Cewar Shugaban Ƙungiyar, Sheikh Abdullahi Bala Lau Daga Jamilu Dabawa
Mahaifiyar Gwamnan Jihar Katsina ta rasu

Mahaifiyar Gwamnan Jihar Katsina ta rasu

Duk Labarai
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIN RAJI'UN: Mahaifiyar Gwamnan Jihar Katsina ta rasu. Allah ya yima Hajiya Safara'u rasuwa yanzu, da asubahin yau lahadi 23/3/2025, mahaifiyar mai girma Gwamnan Malam Dikko Umar Radda PhD CON. Allah ya gafarta mata yasa Aljanna fiddausi ce ce makomar ta. Idan ajalinmu yazo Allah yasa mu cika da imani. Mun samu rahoton rasuwar mahaifiyar Gwamnan daga daya daga cikin jikokin marigayiyar.
Dalibai daga jami’a ta daya a Duniya watau Harvard wadda shuwagabannin kasar Amurka irin su Obama suka yi karatu a cikinta sun zo koyon sanin makamar aiki a matatar man fetur ta Dangote

Dalibai daga jami’a ta daya a Duniya watau Harvard wadda shuwagabannin kasar Amurka irin su Obama suka yi karatu a cikinta sun zo koyon sanin makamar aiki a matatar man fetur ta Dangote

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Dalibai daga jami'ar Harvard ta kasar Amurka wadda kusan itace ta daya a Duniya kuma shuwagabannin kasar Amurkar da yawa irin su Obama can suka yi karatu sun zo matatar man fetur ta Dangote sanin makamar aiki. An ga daliban ana kewayawa dasu inda suke shiga lungu da sako na matatar dan ganin yanda take aiki.
Darajar Naira ta yi rugu-rugu a kasuwar Chanji

Darajar Naira ta yi rugu-rugu a kasuwar Chanji

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Darajar Naira ta yi rugu-rugu a kasuwar Chanji. A wani bincike na tsanaki da aka yi, an gano cewa, Nairar ta fadi a tsakanin 14 zuwa 21 na watan Maris na shekarar 2025. Sannan a kowane sati tana rasa darajar Akalla Naira 18.96. A ranar Juma'ar data gabata, an kulle kasuwar Chanji Naira na da farashin N1,536.89. Wannan a kasuwar Gwamnati kenan. Saidai a kasuwar bayan fage, an kulle kasuwar Naira na da farashin N1,580 akan kowace dala. Wannan bayanai duka an samosu ne daga bayanan canjin kudi daga rubun ajiyar bayanai na babban bankin Najeriya, CBN.