Tuesday, February 17
Shadow

Duk Labarai

CSPR coin zasu raba $10,000 duba yanda zaku samu

Duk Labarai
Ana ci gaba da tara points din CSPR coin wanda yanzu haka yana kasuwa. Zaku iya duba farashinsa a Bybit. Sun canja Wallet ne shine suke neman kowa yayi migrating zuwa sabuwar wallet dinsu, hakanan ba masu rike da coin dinsu kadai ba, ko da baka da coin dinsu sun kawo tasks da ake yi kullun da zaka tara points da yawa. Ba Mining bane, task kawai ake yi Sunce akalla mutum ya tabbatar yana da points guda dubu 10 kamin a raba CSPR coin dashi. Ranar 1 ga watan Nuwamba watau watan gobe kenan za'a yi rabon coin din, wanda bai fara ba a yau in ya dage zai iya tara coin kusan dubu 14. Ga link a kasa ga wanda basu fara ba: https://t.me/csprfans_bot/csprfans?startapp=397188380
Kungiyar ‘yan kasuwar man fetur, IPMAN ta yi baranzanar tsayar da aiki saboda karin kudin man feturninda tace hakan ya kara jefa ‘yan Najeriya wahala

Kungiyar ‘yan kasuwar man fetur, IPMAN ta yi baranzanar tsayar da aiki saboda karin kudin man feturninda tace hakan ya kara jefa ‘yan Najeriya wahala

Siyasa
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Kungiyar 'yan kasuwar man fetur masu zaman kansu ta IPMAN ta yi barazanar daina aiki idan kamfanin mai na kasa,NNPCL bai dakatar da karin kudin man fetur din da yayi ba. Gidajen man fetur mallakin kamfanin man fetur na kasa,NNPCL na fadin Najeriya sun kara farashin man fetur dinsu inda aka rika sayarwa daga Naira 998 zuwa Naira 1070. Hakan yasa kungiyar IPMAN ta bakin wakilinta, Chinedu Ukadike tace basu yi na'am da wannan mataki na karin kudin man fetur din ba inda tace z...
Hotuna: Matashiya me shekaru 16 ta jagoranci zaman majalisar tarayyar Najeriya

Hotuna: Matashiya me shekaru 16 ta jagoranci zaman majalisar tarayyar Najeriya

Siyasa
Kakakin majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya baiwa matashiya me shekaru 16, Ms. Isabel Anani damar zama a kujerarsa ta kakakin majalisa inda ta jagoranci zaman majalisar. Ya bayyana cewa yayi hakanne dan nuna goyon baya ga ranar 'ya'ya mata ta Duniya wadda aka ware dan nuna muhimmanci basu damar yin gwagwarmayar rayuwa da cimma burikansu na rayuwa. Kakakin majalisar ya bayyana cewa, wannan shine karo na farko da hakan ta taba faruwa a tarihin majalisar. Yace an zabo matashiyarne bayan an yi tantancewa ta musamman tsakanin matasa mata kuma ita ce ta yi zarra saboda nuna hali irin na shugabanci da jagorancin Al'umma. Kakakin majalisar ya wallafa hotunan Ms. Isabel Anani a shafinsa na sada zumunta inda yace yayi fatan wannan abu da take yi ya karfafawa sauran matsa gwiwa.
Yadda Yaro Ya Jagoranci Ķìsàn Mai Gidanśa Tare Da Ƙòñe Gawar Šà À Kano

Yadda Yaro Ya Jagoranci Ķìsàn Mai Gidanśa Tare Da Ƙòñe Gawar Šà À Kano

Kano, Tsaro
Daga Anas Saminu Ja'en Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama wasu Matasa Uku da suka haɗar da Aliyu Adamu da Mubarak Abdussalam da kuma Sadik Sunusi da ake zargin su da kisan wani Matashi Dahiru Musa me shekaru 32 a Unguwar Gaida ƴan Kusa, bayan sun gayyace shi har gida suka ba shi shinkafar bera a cikin abinci, tare da caççaka masa wuka har ya mutu daga ƙarshe suka bankawa gawàŕ sa wuta. Kakakin rundunar ƴan Sanda SP Abdullahi Haruna Kiyawa, Ya wallafa Labarin. YADDA ABUN YA KASANCE: Wani ɗan uwan sa da muka sakaye sunan sa, Ya bayyana wa Anas Saminu Ja'en abun da ya faru da Matashin Dahiru Musa wato Alh. Senior mai kimanin shekaru 33 mazaunin Layin Gidan Tsamiya da ke Ɗorayi Gidan Dakali a jihar Kano, Ya ce a ranar Lahadi 29 ga watan Satumbar 2024 Marigayi Baba Alhaji bai kwana...
Gwamnatin Tinubu ta ranto Dala Biliyan 6.45 daga bankin Duniya

Gwamnatin Tinubu ta ranto Dala Biliyan 6.45 daga bankin Duniya

labaran tinubu ayau
A cikin watanni 16 da suka gabata, Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta ranto jimullar kudin da suka kai Dala Biliyan 6.45 daga bankin Duniya. Bayanai sun nuna an ranto kudadenne dan dan gudanar da ayyuka daban-daban a fadin kasarnan. Kuma ana tsammanin nan gaba gwamnatin zata sake ranto wasu kudaden. Da yawan 'yan Najeriya dai na ganin basukan da gwamnati ke ciyowa basu da wani tasiri sosai musamman ganin yanda gwamnatocin baya ke ciwo bashi amma babu abinda ke canjawa. Lamarin ciwo bashi dai ya zama kamar gasa tsakanin gwamnatocin Najeriya inda duk gwamnatin data hau mulki sai ta ciwo bashi a wasu lokutan ma wanda yafi na gwamnatin data gabata. Abin jira a gani dai shine ko wannan gwamnati zata sha banban da sauran gwamnatocin?
Hoto: An kama matar aure, Balkisu Sulaiman da yaron mijinta ya mata ciki bayan ta haihu ta yadda dan a kwata

Hoto: An kama matar aure, Balkisu Sulaiman da yaron mijinta ya mata ciki bayan ta haihu ta yadda dan a kwata

Duk Labarai
An kama matar aure, Barkisu Sulaiman a garin Karaworo,Lokoja jihar Kogi bayan data jefar da dan data haifa a kwata. Matar dai mijinta bashi da lafiya yana kwance yana jinya. Shine aka samu wani daga cikin yaran mijin ya rika lalata da ita har ciki ya shiga. Anan ne dai yaron mijin ya tsere sannan kuma yace bashi ne ya mata cikin ba kuma ta gaggauta zubar da cikin. Tuni dai jama'ar gari suka kamata suka mikata wajan hukumar NSCDC. Jami'in hukumar na jihar Kogi, Paul Igweibuke ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace suna tsare da matar. Mijin Barkisu dai ya samu matsalar ciwon laka watau Spinal Code wanda hakan ne yasa baya iya tabuka komai. Ita kuma bayan da yaron mijin ya mata ciki sai ta jefoshi daga saman bene cikin kwata.
Cin Amana: Ji yanda aka kama wani me unguwa yana baiwa ‘yan Bìnďìgà bayanan sirri a jihar Katsina

Cin Amana: Ji yanda aka kama wani me unguwa yana baiwa ‘yan Bìnďìgà bayanan sirri a jihar Katsina

Katsina, Tsaro
Hukumar 'yansandan jihar Katsina ta kama wani me unguwa me suna Usamatu Adamu dake Runka a karamar hukumar Safana saboda baiwa 'yan Bindiga bayanan sirri. Kakakin 'yansandan jihar, Abubakar Sadiq ya tabbatar da faruwar lamarin a yayin da ake gabatar da masu laifin ga manema labarai. Yace sun samu bayanan me unguwar na da hannu a yin garkuwa da mutane da yawa a jihar. Yace me unguwar na da hannu a satar wasu mutane kamar haka: Abdulkarim, Malam Sakoa, Malam Sirajo, da Ali, wanda suka 'yan kauyen na Runka ne. An kama me unguwar tare da wasu abokan masha'arsa da suka hada da Rabe Sada, wanda aka fi sani da BBC dan shekaru 62, sai kuma Nasiru Sha’aibu dan shekaru 48 wanda dukansu 'yan kauyen na Runka ne.
Hoto: An kama janar din soja inda aka kulleshi a Abuja saboda karkatar da shinkafar tallafi da sayar da motocin aiki da janare na ofishinsa

Hoto: An kama janar din soja inda aka kulleshi a Abuja saboda karkatar da shinkafar tallafi da sayar da motocin aiki da janare na ofishinsa

Duk Labarai
Hukumar sojojin Najeriya ta baiwa manyan janarori shinkafa dan a rabawa kananan sojoji. Saidai Janar Sadiq shi dake kula da sojojin Kano shi yaki rabawa sojojin da yake kula dasu inda ya karkatar da shinkafar. Cikakken sunan sojan shine General M.A. Sadiq kuma jaridar Daily Nigerian tace yanzu haka yana kulle a Abuja. An kuma zargi Janar din da sayar da babban janareta dake wajan horar da sojoji na dajin Falgore dake Kano ga masu gwangwan. Dan haka yanzu an kamashi inda aka mayeshi da Brigadier General A.M. Tukur. A baya dai akwai sojoji da yawa da suka ajiye aiki saboda zargin rashin kwarin gwiwar yin yaki.