Monday, February 16
Shadow

Duk Labarai

TSADAR KUDIN MOTA: Ɗan Agajin Izala Ya Yi Tafiyar Kilomita 161 Da Keke Domin Halartar Wa’azin Ƙasa A Jihar Adamawa

TSADAR KUDIN MOTA: Ɗan Agajin Izala Ya Yi Tafiyar Kilomita 161 Da Keke Domin Halartar Wa’azin Ƙasa A Jihar Adamawa

Duk Labarai
Muhammad Ɗan Liti Dan Agajin izala reshen Jos da ya taso daga karamar hukumar Maiha zuwa Jimeta domin halartar wa'azin ƙasa wanda ya gudana a jiya Asabar. Dan Agajin ya taso ne tun a ranar alhamis ɗin data gabata ne da keken sa, wanda ya ya yadda zango a garin gombi domin hutu da cin abinci. Matashin ya bayyana cewa "ya iso cikin garin Jimeta ne a jiya a Asabar, ya kuma ƙara da cewa ya yi wannan tafiyar ne saboda yanayin da ake ciki na tsadar kuɗin mota". Domin idan a mota ne zan kashe kuɗin da bai gaza 15,000 ba kuma bani dasu a hakan yasa nayi amfani da abinda nake dashi domin halartar wannan wa'azi. Babban abinda ya sa ni zuwa wannan wa'azi shine inada buƙatar sake sayan wasu kayyaki na kayan agaji da kuma sauraren wa'azi, daga cikin kayayyakin da ya ambata a ciki akwai hula...
Gwamnan jihar Akwa-Ibom ya nada diyarsa a matsayin First Lady bayan da matarsa ta rasu

Gwamnan jihar Akwa-Ibom ya nada diyarsa a matsayin First Lady bayan da matarsa ta rasu

Duk Labarai
Gwamnan jihar Akwa-Ibom, Umo Eno ya sanar da diyarsa Helen a matsayin wadda zata zama first Lady a jihar bayan mutuwar matarsa, Pastor Patience Eno. Ya bayyana hakane a yayin da tawagar matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta kai masa ziyarar ta'aziyyar rashin da yayi. Ya bayyana cewa, yana da yakinin diyar tasa zata iya rike wannan mukami yanda ya kamata. Yace zata yi aiki tare da mataimakinsa da kuma kwamishiniyar harkokin mata ta jihar.
Peter Obi yafi kwankwaso nesa ba kusa ba>>Inji Tsohon Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad

Peter Obi yafi kwankwaso nesa ba kusa ba>>Inji Tsohon Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad

Duk Labarai
Tsohon hadimin shugaban kasa,Malam Bashir Ahmad ya bayyana cewa, Peter Obi yafi Dr. Rabiu Musa Kwankwaso a siyasance. Muhawara dai ta kaure a kafafen sada zumunta bayan da Kwankwaso yace yafi Peter Obi tasiri a siyasa inda yace amma duk da haka zai iya zama mataimakinsa. Saidai wannan jawabi nashi ya jawo cece-kuce inda wasu ke cewa hakane wasu ke cewa basu yadda da maganar tashi ba. Tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya bayyana cewa Yana girmama Kwankwaso amma maganar gaskiya a siyasance musamman lura da sakamakon zaben shekarar 2023, Peter Obi yafi Kwankwaso. Kwankwaso dai ya samu kuri'u 1,496,687 wanda kuma a jihar Kanone kawai ya shiga gaba amma Peter Obi ya samu kuri'u 6,101,533 inda kuma ya shiga gaba a jihohi 11.
IKON ALLAH: Ta Asusun Ajiyar Banki (Account) Aka Tura Milyoyin Kudin Fansarsa

IKON ALLAH: Ta Asusun Ajiyar Banki (Account) Aka Tura Milyoyin Kudin Fansarsa

Duk Labarai
Daga Adam Elduniya Shinkafi Yau Asabar 05/10/2024 Allah Ya yi wa yayana Mukhtar Elduniya Shinkafi kuɓuta daga hannun ƴan bindiga bayan ya shafe sama da wata ɗaya a hannunsu. Mun biya maƙuddan kuɗaɗe na fansar sa, bayan shekaranjiya sun bamu account number mun tura masu maira miliyan biyu advance jiya kuma mun kai masu cikon miliyoyinsu. Muna godiya kwarai da gaske ga ƴan uwa da abokan arziki da suka taimake mu da gudunmawar kuɗi da kuma addu'a da masu ba mu shawarwari muna godiya kwarai da gaske ga kowa da kowa. Muna addu'a Allah Ya tsare gaba, Ya tsare mu, Ya baiwa Mukhtar lafiya, Ya kuɓutar da sauran bayin Allah da suke hannunsu, Ya maida mana da alkairi akan abubuwan da muka yi asara, mun karɓi wannan ƙaddara/jarrabawa hannu bibbiyu, mun yarda cewa daga gare ka ne....

Kasar Faransa tace ta daina sayarwa da kasar Israela makakai saboda kashe Falasdinawa

Duk Labarai
Kasar Faransa ta bayyana cewa ta daina sayarwa da kasar Israela makamai saboda kisan Falas-dinawa da kasar ta Israela ke yi. Sanarwar hakan ta fito ne daga kasar ta Faransa bayan da yaki tsakanin Israela da Hamas ya dauki tsawon kusan shekara guda ana yi. Israela dai ta kashe mata da yara da fararen hula da dama a yakin wanda da yawa ke bayyana cewa tanawa Falasdinawan kisan kare dangine. Da yawa sun ji dadin wannan mataki da kasar ta Faransa ta dauka inda rahotanni suka ce Faransar kuma ta yi kira ga sauran kasashen dakw sayarwa Israela makamai su daina. Ta kara da cewa tana son a dauki hanyar diflomasiyya a matsayin wadda zata kawo karshen wannan rikici.
Bayan Shekara Goma Suna Soyayya A Karshe Dai Sun Yi Aure

Bayan Shekara Goma Suna Soyayya A Karshe Dai Sun Yi Aure

Duk Labarai
Bayan Shekara Goma Suna Soyayya A Karshe Dai Sun Yi Aure. Ban taba ganin masoyan da suka rike amana kamar wadannan ba. Sun hadu a FCE Katsina tun a 2014. Bayan kwashe sama da shekara goma suna soyayya, yanzu dai an daura musu aure. Allah Ya sa alkairi ya bada zaman lafiya da zuri'a dayyiba Abokina Jamilu Abubakar J-Star da Amaryar shi Zainab Galadanci. Daga Sulaiman Lawal kamfani

Atiku ya bukaci majalisa ta ƙara wa’adin mulkin Shugaban ƙasa zuwa shekara 6 sannan a mayar da mulkin Najeriya karba-karba tsakanin Kudu da Arewa

Duk Labarai
Atiku ya bukaci majalisa ta ƙara wa’adin mulkin Shugaban ƙasa zuwa shekara 6 sannan a mayar da mulkin Najeriya karba-karba tsakanin Kudu da Arewa Madugun yan adawa a Najeriya Atiku Abubakar, ya rubutawa majalisar dokokin ƙasar nan yana bayar da shawarar a yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima domin mayar da wa’adin mulki zuwa shekara shida ga Shugaban kasa da Gwamnonin jihohi. Takardar da ya aike wa kwamitin majalisar dattawa mai kula da tsarin mulki, Atiku ya kuma bayar da shawarar a mayar da mulkin Najeriya ya koma tsarin karba-karba a matakin Shugaban kasa tsakanin yankunan Arewa da Kudu. Menene ra'ayinku?