Sunday, January 19
Shadow

Siyasa

Babbar Sallah: Gwamnatin jihar Sokoto ta amince a biya albashin watan Yuni

Babbar Sallah: Gwamnatin jihar Sokoto ta amince a biya albashin watan Yuni

Siyasa, Sokoto
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya amince a biya albashin watan Yuni ga ma'aikatan jihar daga ranar Litinin. Gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne domin bai wa ma'aikatan gwamnatin jihar damar yin bikin babbar sallah cikin walwala. Sakataren yaɗa labaran gwamnan Sokoto, Abubakar Bawa, ya ce dukkan ma'aikatan jihar, da na ƙananan hukumomi da kuma ƴan fansho ne za su amfana da wannan karamci. Abubakar Bawa, ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da biyan albashin ma'aikata a kan lokaci, kamar yadda ya ce ya zama al'adar gwamantin, biyan albashi a ranar 20 zuwa 21 na kowanne wata, tun bayan karɓar ragamar mulki. Dama dai gwamnonin jihohin Arewa sun saba yin irin wannan karamci idan aka samu yanayi na gudanar da shagulgulan sallah amma wata bai ƙare ba.
Gwamna Buni Ya Yi Watsi Da ‘Yancin Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi

Gwamna Buni Ya Yi Watsi Da ‘Yancin Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi

labaran jihar yobe state, Siyasa
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi watsi da matakin bai wa kananan hukumomin kasar ‘yancin cin gashin kansu. Buni ya bayyana ra’ayinsa ne jim kadan bayan kada kuri’arsa a zaben kananan hukumomi a mazabar sa da ke Buni Gari. “Lokacin da na hau mulki a shekarar 2019, tunanina shi ne in ba kananan hukumomi cin gashin kai. Sai dai abin takaici shi ne kananan hukumomi shida cikin 17 na jihar Yobe ba sa iya biyan ma’aikata albashi. “Saboda haka, hikimar da ke tattare da wannan asusun hadin gwiwa, wanda ya hada da kokarin kananan hukumomi tare da jihar tare da hadin gwiwa wajen aiwatar da wasu ayyuka, ra’ayi ne da aka samu daga wadannan gazawar,” in ji shi. Gwamnan ya kuma bayyana fatansa game da makomar cin gashin kan kananan hukumomi a Najeriya. "Dimokradiyyarmu tana girma,...
Jihohi 22 sun kashe Naira Biliyan 251 wajan Biyan Bashi a cikin watanni 9

Jihohi 22 sun kashe Naira Biliyan 251 wajan Biyan Bashi a cikin watanni 9

Siyasa
Jihohi 22 a Najeriya sun kashe Naira Biliyan 251.79 wajan biyan bashin da gwamnatocin da suka gada suka bar musu cikin watanni 9 da suka yi suna mulki. Hakanam kuma jihohin sun ciwo bashin Naira biliyan 310.99 a tsakanin wannan lokaci. Sun ciwo wadannan basukanne duk da kudaden da suke samu daga gwamnatin tarayya wanda ake tura musu duk wata. Hakan na kunshene a cikin bayanan yanda kowace jiha ta aiwatar da kasafin kudinta dake runbun tattara bayanai na Open Nigerian States. Jihohin dai sune Abia, Akwa Ibom, Anambra, Benue, Cross River, Delta, Ebonyi, Ekiti, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Niger, Ondo, Osun, Plateau, Rivers, Sokoto, Taraba da Zamfara. Jihohin dai sun gaji jimullar bashin Naira Tiriliyan 2.1 dana dala Biliyan 1.9. Jihohin dai sun gaji basukan a...
Jin dadin Mulkin Tinubu yasa Gwamnatin jihar Sokoto ta sakawa daya daga cikin Titunan jihar sunan dan shugaban kasa, Seyi Tinubu

Jin dadin Mulkin Tinubu yasa Gwamnatin jihar Sokoto ta sakawa daya daga cikin Titunan jihar sunan dan shugaban kasa, Seyi Tinubu

Siyasa, Sokoto
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Ali na fuskantar caccaka daga bakunan da yawa daga cikin 'yan Najeriya bayan sakawa wani titi a jihar Sokoto sunan dan shugaban kasa, Seyi Tinubu. Kafar Peoplesgazette ta bayyana cewa tsohon sunan titin shine Pepsi Road. Tace kuma a ranar 3 ga watan Yuni ne ya kamata a kaddamar da titin amma hakan bata samu ba.
Tunda ake Najeriya ba’a taba yin shugaban kasa me karfin Gwiwa kamar ni ba, na yi abinda shuwagabannin baya suka ji tsoron yi, watau cire tallafin man fetur ba tare da tunanin sake zabe na ba>>Tinubu

Tunda ake Najeriya ba’a taba yin shugaban kasa me karfin Gwiwa kamar ni ba, na yi abinda shuwagabannin baya suka ji tsoron yi, watau cire tallafin man fetur ba tare da tunanin sake zabe na ba>>Tinubu

labaran tinubu ayau, Siyasa
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa shine gwarzon shugaban kasar da ya ajiye kwadayin sake cin zabe gefe guda, bai rufe masa ido ba, yayi abinda ya kamata na cire tallafin man fetur. Ministan yada labarai, Muhammad Idris ne ya bayyana hakan a wani rubutu da yayi a wata jarida ta kasar Ingila. Ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi abinda ya kamata na cire tallafin man fetur. Sannan kuma shugaban ya cire tallafin dala da sauransu dan tayar da komadar tattalin arzikin Najeriya. Cire tallafin man fetur din dai ya jefa 'yan Najeriya cikin halin matsin rayuwa, saidai Minista Muhammad Idris ya bayyana cewa, akwai matakai masu tsari da gwamnatin zata sake dauka nan gaba. “The same has been the case with floating our currency, the Naira – a decision re...
Gwamnatin tarayya ta haramtawa ‘yan mata ‘yan kasa da shekaru 18 shiga Otal

Gwamnatin tarayya ta haramtawa ‘yan mata ‘yan kasa da shekaru 18 shiga Otal

Siyasa, Tsaro
Gwamnatin tarayya karkashin Ma'aikatar mata ta haramtawa Kananan yara 'yan kasa da shekaru 18 shiga otal. Ministar matan, Uju Ohaneye ce ta bayyana hakan inda tace dole duka otal din dake Najeriya dolene su bi wannan umarni. Tace duk Otal din da aka samu bai bi wannan umarni ba zai iya fuskantar hukuncin dakatarwa. Tace an dauki matakanne dan kawar da matsalar safarar 'yan mata. Hakan na zuwane dai a yayin da wasu bidiyon 'yan mata dake da shekarun tsakanin 15 zuwa 16 aka ga an yi safarar su zuwa kasar Ghana dan yin Karuwanci.
Atiku, Kwankwaso: Dalilan Da Ya Sa Arewa Ba Za ta Iya Magana Da Murya Ɗaya Ba A 2027 – Buba Galadima

Atiku, Kwankwaso: Dalilan Da Ya Sa Arewa Ba Za ta Iya Magana Da Murya Ɗaya Ba A 2027 – Buba Galadima

Siyasa
Atiku, Kwankwaso: Dalilan Da Ya Sa Arewa Ba Za ta Iya Magana Da Murya Ɗaya Ba A 2027 – Buba Galadima. DAGA: Abbas Yakubu Yaura Wani jigo a jam’iyyar, NNPP, Buba Galadima ya ce ba zai taba yiwuwa ɗaukacin yankin Arewa su samu ɗan takarar shugaban ƙasa ɗaya a zaɓen 2027 ba. A wata hira da jaridar Sun, tsohon sakataren rusasshiyar jam'iyyar CPC, ya bayyana cewa a tsarin dimokuradiyya irin na Najeriya, masu zaɓe na da ƴancin yin zaɓi daban-daban. Da aka tambaye shi ko ƴan Arewa za su zaɓi Atiku Abubakar, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, ko kuma takwaransa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, Galadima ya ce, “Ba ma cikin còci; Ba ma cikin másallaci. Me ya sa za mu yi magana da murya ɗaya? “Dimokradiyya kenan."Idan ka haɗa mutane uku tare, kowa ya sami hanyar t...
Kalli Bidiyo: Kalli ya da jama’ar kasar Burki na Faso ke lakadawa tsohon Ministansu duka bayan samunsa da sace makudan kudade

Kalli Bidiyo: Kalli ya da jama’ar kasar Burki na Faso ke lakadawa tsohon Ministansu duka bayan samunsa da sace makudan kudade

Siyasa
Bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumuna na tsohon ministan sufuri a kasar Burkina Faso,Vincent Dabilgou inda aka ga mutane na zaneshi. An masa hakane bisa zargin cewa ya saci makudan kidade a kasar. https://twitter.com/PSAFLIVE/status/1799334263747465694?t=utEYAEYbq_Y905R_nO6sWA&s=19 Lamarin dai ya dauki hankula sosai inda da yawa suka rika cewa sun yi fatan a kasarsu ma za'a iya yin hakan
Gwamnatin jihar Kano ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ilimi

Gwamnatin jihar Kano ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ilimi

Kano, Siyasa
Gwamnatin jihar Kano ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ilimi a faɗin jihar a wani mataki na farfaɗo da ɓangaren ilimin jihar. Yayin da yake jawabi a wani taro da gwamnatin jihar ta shiyya, gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf ya ce matakin ya zama wajibi domin magance matsalolin da ɓangaren ilimin jihar ke fuskanta. Gwamnan ya kuma yi kira da sauran masu ruwa da tsaki a ɓangaren ilimin jihar su fito su haɗa ƙarfi domin magance matsalolin da suka yi wa ɓangaren ilimin jihar katutu. ''Ina Kira ga masu ruwa da tsaki da gwamnati da malamai da iyaye da kamfanoni masu zaman kansu da sauran al’umma, su haɗa kai, wajen farfaɗo da fannin ilimi, domin ci gaban al’ummarmu'''. ''Samun ilimi mai inganci shi ne babban makami mafi inganci na yaƙi da talauci da miyagun laifuka cikin al'ummarmu''. Gwamn...