Sai an shekara 6 ana shan wahalar da cire Tallafin man fetur ya kawo>>Inji Shugaban ADC
Shugaban jam'iyyar ADC, Dr Ralphs Okey Nwosu ya bayyana cewa, sai an shekara 6 ana wahala kamin a kawo karshen wahalar da cire tallafin man fetur ya jefa mutane.
Ya bayyana hakane hirar da Daily Trust ta yi dashi.
Cire tallafin man fetur ya jefa mutane da yawa a cikin matsin rayuwa inda mutane suka rika fama da abinda zasu ci wanda a baya ba haka bane.
Saidai Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, wannan mataki ne data dauka dan amfanar al'umma baki daya wanda kuma na dolene.