Na sadaukar da kaina a turani zuwa Duniyar wata a matsayin dan Najeriya na farko>>Sanata Ben Murray Bruce
Sanata Ben Bruce ya jinjinawa gwamnatin tarayya kan sakawa yarjejeniyar zuwa duniyar wata hannu tsakanin Najeriya da kasar Amurka.
A jiya ne dai hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya ta tabbatar da cewa, an sakawa yarjejeniyar hannu kuma za'a tura dan Najeriya na farko zuwa sararin samaniyar.
https://twitter.com/benmurraybruce/status/1803543591341662332?t=VOMxw7MsbkJf_xDOf49lzw&s=19
Sanata Bruce yace ya sadaukar da kansa a matsayin dan Najeriya na farko da zai fara zuwa Duniyar watar.
Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta.