Friday, June 26
Shadow

Da ace tintuni da sabon taken Najeriya ake amfani da ba’a samu matsalar tsaron da ake fama da ita ba>>Inji kakakin majalisar tarayya Akpabio

Kakakin majalisar tarayya, Godswill Akpabio ya bayyana cewa, da tuntuni da sabon taken Najeriya ake amfani, da ba’a yi fama da matsalar ‘yan Bindigar da ake fama da ita ba.

Ya bayyana hakane a wata ziyara da ya kai wata tsangayar karatun Dimokradiyya a Abuja ranar Talata.

Ya kara da cewa saboda idan aka lura da taken yana sawa mutum soyayyar makwabcinsa wanda idan mutum na son makwabcinsa ba zai cutar dashi ba.

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya canja taken Najeriya daga wanda aka sani zuwa wannan sabon wanda ya jawo cece-kuce sosai.

Karanta Wannan  Lokacin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai na gwamnan Kaduna an cire Naira Biliyan 423 daga asusun bankin jihar ba tare da yin wani aiki da kudin ba>>Majalisar Jihar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *