Duk Wani Jami’in Zabe Da Ya Aikata Cin Hanci Da Rashawa Da Rashin Da’a Zai Fuskanci Hukunci — INE
INEC ta gargadi jami'anta Gabanin zaben gwamnonin da za a yi a ranakun 21 ga watan Satumba da 16 ga watan Nuwamba, 2024 a jihohin Edo da Ondo.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi gargadin cewa duk wani ma’aikacin hukumar da ya aikata cin hanci da rashawa da rashin da’a zai fuskanci hukunci mai tsanani a karkashin doka.
Daga: Abbas Yakubu Yaura