Tuesday, September 17
Shadow

Yanzu-Yanzu:EFCC ta kafa kwamiti dan binciken tsohon gwamnan jihar Kaduna malam Nasiru Ahmad El-Rufai

Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ta kafa wani kwamiti na musamman dan binciken zargin da akewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai kan satar Naira Biliyan 423.

Za’a binciki tsohon gwamnan ne tare da wasu manyan da suka yi aiki tare da shi a gwamnatinsa.

Nan gaba kadan ake sa ran EFCC din zasu gayyaci El-Rufai dan binciken sa.

Hukumar ta EFCC tace sun karbi korafi dake bukatar a bincike tsohon gwamnan na jihar Kaduna.

za a bincike gwamnan ne tare da sauran mukarrabansa da suka yi aiki tare dashi tsakanin shekarau takwas daya yi akan karagar mulki.

Karanta Wannan  Mutane na cikin wahala da Yunwa a Najeriya>>Obasanjo

Cikin wadanda za a bincika hadda ma’aikatan KADRIS KADRA amma banda injiniya Amina jafar Ladan wadda aikin wata daya kacal tayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *